Takaitattun Labaran Duniya Na Safiyar Laraba 10/09/1445AH – 20/03/2024CE

Screenshot 20240317 131846 com.whatsapp.w4b edit 21836918129479

Daga Baba Usman Gama

Majalisar Wakilai ta bayar da wa’adin mako hudu na tabbatar da an nemo wadanda suka kashe sojojin Najeriya 17 a Jihar Delta.

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya ce yana ganin kamar baƙi daga ƙetare ne suka hallaka sojojin Najeriya 17 a Jihar Delta.

Kwamitin Majalisar Wakilai kan yaƙi da cutar maleriya da kanjamau da tarin fuka, na neman Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate da ya bayyana a gabanta kan zargin almundahanar dala miliyan 300.

Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) ta ce fasinjoji 10 ne suka mutu a wani hatsarin mota a titin Kaduna- Abuja.

Sojoji sun kuɓutar da jarirai 2 da mata 5 da aka yi garkuwa da su a Zamfara.

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ce nan ba da jimawa ba gwamnatinsa za ta fara rabon tallafin kayan abinci ga jami’an tsaron da ke Jihar.

‘Yan bindiga sun aikata kazamin kisa kan masu shirin buɗa baki a Zamfara.

Sama da mutum 300 sun kamu da cutar kwalara a jihar Ribas.

‘Yan sandan Brazil suna tuhumar tsohon shugaban ƙasar Bolsonaro da laifin aikata zamba dangane da bayanan riga kafinsa na cutar korona.

Tunisiya ta rufe iyakarta da Libya saboda hare-haren ƴan ta’adda.

Daya daga cikin masu kungiyar Manchester United Sir Jim Ratcliffe na son a maye gurbin kocinsu Erik ten Hag da kocin Ingila Gareth Southgate.

Manchester City na iya bai wa Grealish damar barin kungiyar yayin da suke kokarin hada kuɗin inganta tawagar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

One Reply to “Takaitattun Labaran Duniya Na Safiyar Laraba 10/09/1445AH – 20/03/2024CE”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *