Takaitattun Labaran Duniya Na Safiyar Laraba 13/06/1445AH – 27/12/2023

best seller i2

Daga Baba Usman Gama

Shugaba Tinubu ya ba da umarnin cafko wadanda suka kashe mutane sama da 140 a Filato.

Majalisar tarayya tana fatan a kammala zama a kan kundin kasafin kudin 2024 kafin karshen shekarar bana.

Fursunoni uku, ciki har da wani dan fashi da wanda aka yanke wa hukuncin kisa sun tsere daga gidan yari na Ijebu Odeda da ke Jihar Ogun.

Allah Ya yi wa tsohon kakakin Majalisar Wakilai, Ghali Umar Na’Abba rasuwa, ya rasu yana da shekara 65 a duniya.

Rundunar ƴan sandan jihar Neja ta kama wani ƙasurgumin ɗan ta’adda da ya addabi al’ummar jihar da kuma wata ɗaliba ƴar shekara 18 mai ba ƴan bindiga bayanai.

Houthi da Hezbollah sun sake kai hare-hare kan Isra’ila.

Sweden na daf da shiga ƙungiyar NATO.

Iran ta ƙara yawan makamashin Uranium da take samarwa.

Shugaban kasar Cuba ya ce ƙasarsa ba za ta taɓa kasancewa cikin masu halin ko-in-kula ba, tana ɗaga murya don kare Falasɗinu, akai-akai.

Rundunar sojin Isra’ila ta ce akalla sojoji 40 ne suka jikkata a fadan da aka gwabza a Gaza cikin sa’o’i 24 da suka gabata.

EPL: Manchester United ta sami nasara akan Aston Villa da ci 3:2 a wasan jiya.

EPL: Liverpool ta sami nasara akan Bunley da ci 2:0 a wasan jiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *