Takaitattun Labaran Duniya Na Safiyar Litinin 08/01/2024 – 26/06/1445AH

best seller i2

Daga Baba Usman Gama

Shugaba Tinubu ya amince a biya Super Eagles da wasu ‘yan wasan Nijeriya bashin biliyan 12.

‘Yan majalisa sun ware karin N30bn da nufin a gyara zauren majalisar tarayya a cikin kundin kasafin kudin 2024.

Dakarun Operation Hadin Kai sun kashe ƴan ta’adda da dama a wani samame da suka kai a sassan jihar Borno.

‘Yan bindigar da sukayi garkuwa da Alh. Mansoor Al-Kadriyar da yayansa 6 sun suka bukaci a biya kudin fansa naira miliyan 60.

NDLEA, ta ce ta kama wata mata yar shekara 28 mai suna Bilkisu Suleiman wacce ke kai wa yan bindiga harsashi.

An bayyana sunayen mutum bakwai da dayan su zai zama Ohinoyi na Ebiraland.

‘Kashi 40 na mutane kaɗai suka fita kaɗa kuri’a a zaɓen Bangladesh’

Majalisar Dokokin Amurka ta amince da sama da Dala Triliyan 1 kasafin kudin 2024.

Kylian Mbappe, ya cimma yarjejeniyar tafiya Real Madrid a ƙarshen kwantiraginsa da PSG amma kuma duk da wannan yarjejeniya Mbappen zai iya sauya shawara ya tafi gasar Premier.

FA Cup: Manchester City ta sami nasara akan Huddersfield da ci 5:0 a wasan jiya.

Copa del Rey: Barcelona ta sami nasara akan Barbastro da ci 3:2 a wasan jiya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *