Takaitattun Labaran duniya na Safiyar Litinin 27/11/2023 – 12/05/1445AH

best seller i2

Daga Baba Usman Gama

Ministan shari’a Lateef Fagbemi (SAN) ya bukaci ā€˜yan kasa da su goyi bayan ayyukan gyara kasa na Shugaba Tinubu.

Haramta holewa a gidan Gala da sauran wuraren rage dare da Hukumar Hisbah ta ce suna kara habaka ayyukan lalata ya janyo cece kuce a Jihar Jigawa a tsakanin wadanda haramcin ya shafa.

Akalla mata dubu ne su ka yi zanga-zanga a titunan garin Kano domin nuna rashin jin dadinsu game da hukuncin shari’ar zabe.

Gwamna Alex Otti na jihar Abia ya watsar da sabon gidan gwamnatin jihar na biliyoyin nairori tun bayan hawanshi mulki inda yake gudanar da mulki daga kauye.

Bayan ā€˜yan bindiga sun sace mai sarautar gargajiya a yankin Otulu a jihar Imo, daga bisani an tsinci gawarsa a bakin hanya.

An sako wani dan Jamus da ake garkuwa da shi a Mali.

Dubbai mutane sun yi tattaki kan nuna wa yahudawa kiyayya a Landan.

Kasashe na kiraye-kirayen ganin an tsawaita yarjejeniyar Isra’ila da Hamas.

EPL: Manchester United ta sami nasara akan Everton da ci 3:0 a wasan jiya.

Laliga: Real Madrid ta sami nasara akan Cadiz da ci 3:0 a wasan jiya.

Seria A: Juventus da Inter Milan sun tashi 1:1 a wasan jiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai šŸ‘‡šŸ‘‡

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *