Takaitattun Labaran duniya na Safiyar Litinin 30/10/2023 – 15/04/1445AH

best seller i2

Daga Baba Usman Gama

Rundunar ‘yan sandan jihar Benue ta kama wani magidanci mazaunin Korinya-City dake karamar hukumar Konshisha da ake zargin ya kashe matarsa.

Ana ci gaba da aikin gano mutane 104 da jirgin ruwa ya kife da su a Taraba

Wasu fusatattun matasa sun jikkata wani Fasto da hadiminsa kan zargin satar mazakutar wani matashi a Makurdi da ke jihar Benue.

Gobara ta kone shaguna a kusa da babban masallacin Zariya.

’Yan Shi’a sun bukaci Najeriya ta yanke alaka da Isra’ila.

’Yan bindiga sun kashe ma’aurata da malamin firamare a Kaduna.

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz said ya ce kasarsa na son saka jari a fannin iskar gas da ma’adanai a Najeriya.

An yi mummunan artabu tsakanin mayakan Hamas da sojojin Isra’ila a Gaza.

Rundunar Sojin Ruwa ta Turkiyya ta yi fareti mafi girma a tarihinta da jiragen yaki dari domin bikin cikar kasar shekara 100 da zama Jamhuriya.

Sabon rikicin kabilanci ya sa dubban mutane sun tsere daga gidajensu a Ghana.

An zabi Joshua Osih a shugabancin jam’iyyar SDF a Kamaru.

Kungiyar Turai ta ba da motocin sulke 100 ga kasar Ghana.

Isra’ila ta lalata masallatai 47 da coci 3 a Gaza.

Laliga: Atlentico Madrid ta sami nasara akan Deportivo Alves da ci 2:1 a wasan jiya.

Seria A: Inter Milan ta sami nasara akan Roma da ci 1:0 a wasan jiya.

Seria A: Ac Milan da Napoli sun tashi 2:2 a wasan jiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *