An kona zauren majalisar dokokin jihar Ribas Bayan Barazanar Tsige Gwamna
Alfijir Labarai ta rawaito wannan ya zo ne a daidai lokacin da ake ta rade-radin shirin tsige Gwamna Similanayi Fubara.
Maharan sun samu shiga majalisar dokokin ne a daren ranar Lahadi inda suka kona ta.
Rahotanni na nuni da cewa daukin gaggawar da jami’an kashe gobara suka yi ne ya hana gobarar bazuwa a harabar majalisar baki daya.
Kokarin da aka yi na zantawa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ribas, SP Grace Iringe Koko ya ci tura a lokacin da ake gabatar da wannan rahoto.
An tsaurara matakan tsaro a harabar ginin yayin da jami’an kashe gobara ke fafatawa don shawo kan gobarar.
Sai dai wani rikici ya barke a majalisar dokokin jihar Ribas a ranar Litinin yayin da majalisar ta cire Edison Ehie a matsayin shugaban masu rinjaye.
Edison Ehie babban mai goyon bayan Gwamna Similanayi Fubara ne, sun bayyana cewa ya ba da kunya ga yunkurin tsige gwamnan.
Da yake sanar da tsige shugaban masu rinjaye a majalisar da ke zamanta a Fatakwal, babban birnin jihar, kakakin majalisar, Martins Amaehwule, ya ce an tsige shi ne saboda rashin halartar zaman majalisar.
Amaehwule yace kimanin yan majalisar 17 ne suka goyi bayan tsige dan majalisar.
A halin da ake ciki dai hukumomin tsaro sun mamaye harabar majalisar baki daya.
Wasu da ba a san ko su waye ba sun kona zauren Majalisar.
Rahotanni na nuni da cewa hakan ya faru ne da nufin dakile shirin tsige gwamnan, wanda rahotanni suka ce ya samu sabani da magabacinsa kuma ministan babban birnin tarayya (FCT), Nyesom Wike.
Daily Trust
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp