Daga Baba Usman Gama.
Gwamnatin tarayya ta ce za ta kwace lasisin kamfanonin rarraba wutar lantarki.
Kotun Daukaka Kara ta sanya gobe Juma’a domin yanke hukunci a kan zaben gwamnan Jihar Kano, tsakanin Abba na NNPP da Gawuna na APC.
Kotun ɗa’ar ma’aikata ta bayar da belin Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado.
Majalisar wakilai ta kori wakilan hafsoshin tsaron kasar da suka halarci taron da suka kira domin tattauna batutuwan da suka shafi tsaron kasa.
DSS ta sake gurfanar da Husseni Isma’il da ake zargi da hannu a harin bam kan masallacin Kano.
Dubun wani mutum mai ba ƴan ta’addan ISWAP bayanai ta cika a ƙaramar hukumar Monguno ta jihar Borno.
Majalisar dokokin jihar Taraba ta rage wa’adin shugabannin kananan hukumomi daga shekaru uku zuwa shekaru biyu a jihar.
Gwamnatin jihar Filto, ta kafa wani kwamiti da zai yi bincike don gano yadda aka yi ma’aikatan hukumar alhazan jihar suka yi zambar naira miliyan 200.
Gwamnatin jihar Enugu ta amince da biyan dubu 10 zuwa 25 ga ma’aikata don rage musu radadin cire tallafin mai a kasar.
.An tarwatsa masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a Kaduna.
Wasu miyagun ƴan bindiga sun kashe wani malamin cocin (ECWA) Fasto David Musa a jihar Kogi.
Shugaban Malawi ya haramtawa kansa da jami’ansa tafiya kasashen ketare.
Domin Kallon Shirin FATAKE Mai Dogon Zango Season 1 Da Kuma CIgaba Da Kallon Season 2, Danna wannan Link din👇
https://youtube.com/@ukentertainmentkano?si=PPtuxJz76OuNP_oI
Kayan abinci sun kare a sansanin ‘yan gudun hijirar Sudan da ke Chadi.
Afrika ta Kudu ta maka Isra’ila a Kotun Duniya kan yakin Gaza.
An rantsar da mambobin hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Nijar.
Shugaban adawar Isra’ila ya buƙaci Netanyahu ya sauka.
An kashe sojojin Isra’ila 50 a rikicin Gaza.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp