Ganduje da Abdullahi Abbas na shirin tayar da tarzoma a Kano – In Ji NNPP.

Jam’iyyar NNPP ta yi kakkausar suka kan wani shiri da shugaban jam’iyyar APC na kasa kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ta bankado na tayar da zaune tsaye a Kano, bayan hukuncin kotun daukaka kara.

Alfijir Labarai ta rawaito wata sanarwa da ya fitar a Abuja, shugaban NNPP na kasa, Hon. Abba Kawu Ali ya ce Ganduje da tawagarsa na shirin shirya tashin hankali a jihar Kano.

“Muna samun tabbataccen labari, cewa Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje da Shugaban Jam’iyyar APC reshen Jihar Kano, Abdullahi Abbas, sun ba da umarnin aike da ’yan baranda da za a dauka aiki a wasu muhimman wurare a cikin babban birnin da manufarsu ta tada rikici a Kano idan hukuncin kotun daukaka kara bai yi musu ba.”

Shugaban jam’iyyar NNPP na kasa ya tunatar da mutane aukuwar irin haka a lokacin babban zaben shekarar 2023, inda aka tara ‘yan daba domin tayar da tarzoma a wurare daban-daban a cikin Jihar ciki har da Sakatariyar NNPP da ke karamar hukumar Tudun Wada inda aka kona ‘ya’yan jam’iyyar sama da 10 da ransu.

Domin Kallon Shirin FATAKE Mai Dogon Zango Season 1 Da Kuma CIgaba Da Kallon Season 2, Danna wannan Link din👇

https://youtube.com/@ukentertainmentkano?si=PPtuxJz76OuNP_oI

Don haka jam’iyyar ta yi kira ga dukkanin hukumomin tsaro da su gaggauta dakile wannan mugun nufi da kuma tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a jihar.

“Abin takaici ne, yadda shugabannin jam’iyyar APC na kasa da na Jihohi duk sun tashi tsaye wajen haifar da rikici a yanayin da ya kamata su kare ko ta halin kaka,” in ji Abba Kawu.

Muna kira ga daukacin magoya bayan jam’iyyar NNPP da na jihar Kano da su kwantar da hankulansu, kuma su kasance masu bin doka da oda a gaban kotun daukaka kara da kuma bayan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke domin muna da kyakkyawan fata na adalci.

Jam’iyyar NNPP a matsayinta na jam’iyyar zaman lafiya, ta yi imanin cewa ba za a iya samun ci gaba a cikin yanayi na hargitsi da tashin hankali ba, don haka ta nanata kira ga hadin kan magoya bayanta da mutanen jihar Kano da su tabbatar da zaman lafiya tare da kai rahoton duk wani abin da ake zargi ga hukumomin tsaro.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *