Takaitattun Labaran Duniya Na Yammacin Alhamis 18/09/1445AH – 28/03/2024CE

IMG 20240103 WA0021

Daga Baba Usman Gama

Rundunar Sojoji ta fitar da sunayen wadanda ake zargi da kashe Sojoji a jihar Delta.

Kamfanin mai na Najeriya, NNPCL ya ƙaryata rahotannin da ake yaɗawa na rage farashin mai daga naira 568 zuwa 560 duk lita ɗaya.

‘Yan sanda sun kashe ‘yan bindiga 2 a Benuwe.

Rundunar ’Yan Sandan jihar Kano, ta cafke wasu riƙaƙƙun ’yan daba 22 da suka addabi unguwar Dorayi da ke Karamar Hukumar Gwale a jihar.

Kotu ta tsare wani mutum kan yi wa ‘yar shekaru 11 ciki a jihar Legas.

Wani matashi mai shekara 25 ya rasa ransa a yankin Magama-Gumau na Karamar Hukumar Toro da ke jihar Bauchi sakamakon caka masa wuka a wuyansa.

Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya haɗa daliban makarantar Kuriga 137 da aka sace da iyalansu.

Babban jami’in Binance da ake tsare da shi Tigran Gambaryan, ya maka mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu, da hukumar EFCC ƙara a gaban kotu.

Wasu gungun ƴan bindiga kimanin 30 sun ƙona ofishin ƴan sanda na garin Neni da hedkwatar ƙaramar hukumar Anaocha a jihar Anambra.

An samar da wata mota a Masallacin Harami, da za a riƙa ɗaukar dattijai da masu rauni domin gudanar da aikin Umrah a cikin sauƙi.

An sayar da ƙofar da jarumar da ta fito da suna Rose a cikin fitaccen fim ɗin Titanic ta haye bayan kifewar jirgin ruwan da ya ɗauko su kan Dala 718,750.

Gidauniyar Sarkin Saudiyya, Salman Ibn AbdulAziz ta raba kayan abinci ga gidaje fiye da 2,000 a jihar Kano.

An tsawaita dokar taɓaci kan masu iƙirarin jihadi a Burkina Faso.

China ta fara kera mota mai amfani da lantarki.

Mahaukaciyar guguwa ta afka arewacin Madagascar.

Shugaban Uganda ya ƙaddamar da bankin Musulunci na farko a ƙasar.

Masu shigar da kara a Spain sun nemi kotu ta aike da Rubiales gidan yari.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *