Daga Baba Usman Gama
Shugaba Tinubu ya ba da umarnin sake dawo da tsarin ciyar da ɗaliban makaranta dan magance ƙalubalen rashin zuwan yara makaranta.
Lauyan INEC ya tabbatarwa kotun koli cewa kuri’un da aka soke a shari’ar Gwamnan Kano ba na haram ba ne, daga hannun hukuma su ka fito.
Tsohon shugaban kasa Buhari ya jagoraci rabon tallafin kudi ga marayu da Gwamnan Katsina Umar Dikko Radda ya yi, a garin Daura.
Kotun ƙoli za ta sanar da ranar yanke hukuncin ƙarshe kan zaɓen gwamnan Kano da kuma Bauchi.
Majalisar dattawa ta amince da naɗin alkalai 11 na Kotun Koli.
Majalisar Dokoki ta gayyaci tsohon ministan jiragen sama Hadi Sirika kan badakalar jiragen sama.
Majalisar dokokin Sokoto ta amince a kafa rundunar tsaron al’ummar jihar.
Biyo bayan samun ingantaccen rahoto, rundunar ‘yan sanda ta samu nasarar gano wasu makamai da aka boye su a cikin wani buhu a jihar Delta.
Matatar Mai Ta Fatakwal ta fara aikin gwaji bayan shafe shekaru ba ta aiki, duk da kudaden da Gwamnatin Tarayya ta yi ta kashewa domin farfaɗo da ita.
Gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da wani matashi a gaban babbar kotun jihar kan zargin caka wa abokinsa wuka a ciki.
Gwamnatin jihar Filato zata fara rijistar masu keke NAPEP.
Wani lauya ya shiga hannun ’yan sanda kan zargin lakadawa matarsa dukan kawo wuka a jihar Akwa Ibom.
‘Yan awaren Abzinawa sun sanar da kwace ikon arewacin Mali.
Benin ta sanar da shirin dawo da alaka tsakaninta da Nijar bayan juyin mulki.
Mutane da dama sun mutu bayan wani artabu a yankin Arewa mai Nisa a Kamaru.
Kotu ta wanke Ba’amurke daga laifin kisa bayan shafe shekaru 48 a gidan yari.
Kungiyar Hamas ta harba rokoki zuwa Isra’ila sannan sunce ba zasu ƙara sakin ƴan Isra’ila da suke garkuwa da su ba sai an tsayar da yaƙi.
Ba za mu ƙara sakin ƴan Isra’ila da muke garkuwa da su ba sai an tsayar da yaƙi’.
An soma ƙirga ƙuri’un da aka jefa a zaɓen Congo.
Kotun Turai ta ce FIFA da UEFA sun karya dokar EU wajen hana kafa gasar Super League.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp