Takaitattun Labaran Duniya Na Yammacin Juma’a 15/06/1445AH – 29/12/2023

best seller i

Daga Baba Usman Gama

Shugaban ‘yan sanda ya kai ziyara Filato a kan hare-haren jajiberen Kirsimeti.

Hukumar kula da aikin ‘yan sanda ta koka kan abin da ta kira rashin nuna ƙwarewa da ƴan sandan sarauniya ko kuma ‘yan sandan sa-kai ke nunawa, a ƙoƙarin da suke yi wajen tallafa wa tsaron al’umma.

Gwamnan Kano ya kaddamar da soma aikin gina Gadojin sama a Dan’agundi da Tal’udu dake jihar.

Akalla ‘yan sanda 2 aka kashe tare da garkuwa da wasu mutane a yayin da ‘yan bindiga suka kai hari a jihar Anambra.

Jigon jam’iyyar NNPP, Razaq Aderibigbe, ya bayyana kwarin guiwar cewa kotun koli zata yi adalici a shari’ar zaben gwamnan Kano.

Kungiyar Middle-Belt Forum ta ce ‘yan ta’adda sun rubuto wasika cewa za su kuma kai wani hari a jihar Filato.

Yan bindiga sun kashe ‘yan sanda 2 yayin da suka kai hari kan ayarin jagoran PDP a jihar Anambra, Chris Uba.

Wasu masu safarar tabar wiwi da sauran miyagun kwayoyi sun shiga hannun NDLEA a Jihar Yobe.

’Yan bindiga na barazanar kashe daliban Jami’ar Gusau nan da kwana 7 idan ba’a biya musu bukatunsu ba.

Kotu ta hana PDP kwace kujerar ‘yan majalisar Rivers 27 da suka sauya sheka zuwa APC.

Boko Haram ta sake tarwatsa turakun raba wutar lantarki a Borno.

Mutum 16 sun mutu a luguden wutar da Rasha ta yi a yankunan Ukraine

Wata ‘yar Ghana mai son shiga kundin tarihi ta shafe kwana biyar tana rera waƙa.

Shugaban ƙasar Burundi yace Kamata ya yi a riƙa jefe ‘yan luwadi.

MDD ta mika ikon sansanin Timbuktu ga hukumomin Mali.

Iran ta rataye wasu mutane 4 da ke yiwa Isra’ila aikin leken asiri.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *