Daga Baba Usman Gama
Gwamnatin Tarayya ta umarci Babban Hafsan Soji da ya tura karin dakaru zuwa Zamfara Katsina, Kaduna da Sakkwato domin dakile hare-haren ’yan bindiga.
Sheikh Dokta Abdallah Gadon Ƙaya, ya shawarci Gwamnan Kano da makusantansa, da su kai zuciya nesa su kira Malam Daurawa su ba shi haƙuri.
Fursunoni a wannan Juma’ar sun gudanar da zanga-zanga a gidan gyaran halin Jos da ke Jihar Filato saboda yunƙurin mahukunta na rage musu kasafin abinci.
Akalla mutum 6 ne suka rasu sakamakon kamuwa da cutar sanƙarau a Kananan Hukumomin Nafada da Funakaye a Jihar Gombe.
Fitacciyar jarumar nan ta dandalin TikTok, Murja Ibrahim Kunya, ta yi ƙarar Gwamnatin Kano a gaban Babbar Kotun jihar.
Najeriya ta buƙaci kamfanin Binance ya biya ta diyyar dala biliyan 10.
Likitoci 38 a Kasar Saudiyya sun kwashe awanni suna aikin raba tagwaye ‘yan Najeriya da aka haifa a manne da juna.
Kotu a Somalia ta yanke hukuncin kisa ga wasu ‘yan Morocco shida da ke aiki da kungiyar IS.
Jana’izar Navalny ta zama taron ‘yan adawa mafi girma cikin shekara uku a Rasha.
AU ta aike da ta’aziyya ga iyalen madugun adawar Chadi.
Shugaban RSF na Sudan ya je Libya don tattaunawa kan rikicin ƙasar.
Za a gudanar da zaɓe na farko a Iran tun bayan zanga-zangar ƙin jinin gwamnati.
An katse wa majalisar dokokin Ghana lantarki saboda bashin kuɗin wuta.
Kocin tawagar Super Eagles ta Najeriya, Jose Peserio ya sanar da murabus daga mukaminsa.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V