Takaitattun Labaran Duniya Na Yammacin Juma’a 26/01/2024CE – 14/07/1445AH

IMG 20240103 WA0021

Daga Baba Usman Gama

Dakarun Sojoji sun yi nasarar hallaka wasu ‘yan bindiga uku a Karamar Hukumar Karim Lamido da ke Jihar Taraba.

Kotun ƙoli ta tabbatar da hukuncin ɗaurin shekara biyar kan Farouk Lawan.

Hukumar Kashe Gobara ta Kano, ta ceto wani matashi mai shekara 37 da ya yi kokarin rataye kansa kan bashin miliyan biyu da ake bin sa.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa, ta kama wasu mutum uku kan zargin satar awaki 48 a Kananan Hukumomin Babura da Kiyawa na jihar.

An kama ‘ya’yan mista Ibu kan zargin satar gudunmawar miliyan 55 da ya samu na jinyarsa.

Mai magana da yawun Gwamnan Kano Sanusi Dawakin Tofa, yace gwamnan na Kano ba shi da wata matsaya ta barin jam’iyyarsa ko Æ™in bari a yanzu.

Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas ya rantsar da kwamishinoni tara da ya sake naÉ—awa a karo na biyu bayan sun yi murabus.

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin kabilar Jukun ne sun kai hari Wukari jihar Taraba sun kashe ‘yan gudun hijira da dama.

‘Yan bindigar da suka yi garkuwa da mutum 31 a yankin Ƙaramar Hukumar Batsari ta jihar Katsina sun nemi abiya su Naira miliyan 60 kafin su sakesu

Babbar Kotun Tarayya da ke jihar Legas ta yanke wa Fasto Feyi Daniels hukuncin daurin rai da rai bisa laifin cin zarafi da kuma fyade.

Kotun Duniya tace dole ne Isra’ila ta dakatar da kisan Æ™are dangi.

Kungiyar Hamas ta ce tana maraba da hukuncin da kotun duniya ta yanke na umurtar Isra’ila ta dauki dukkan matakan dakatar da duk wani abu da ya shafi kisan Æ™are dangi a Gaza.

Kotu a Kenya ta hana gwamnati aikewa da ‘yan sandan kasar zuwa Haiti.

ECOWAS ta É—age aikewa da tawaga zuwa jamhuriyar Nijar.

Dawan wasan Najeriya Moses Simon ya ce suna sane da yadda Kamaru ke saka karfi wajen buga wasa, yana mai cewa sun tattauna hakan a tsakaninsu ‘yan wasa.

Kocin Kungiyar Kwallon Kafa ta Liverpool, Jurgen Klopp ya sanar cewa zai bar kungiyar a karshen kakar wasanni ta bana.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *