Takaitattun Labaran Duniya Na Yammacin Laraba 03/01/2024 – 21/06/1445AH

IMG 20240103 WA0021

Daga Baba Usman Gama

Shugaban Hukumar ICPC Musa Aliyu ya gana da dan jaridar Daily Nigerian kan badakalar da ya bankado a wata jami’a a Benin.

EFCC ta titsiye Halima Shehu ta hukumar NSIPA mai ba da tallafin dogaro da kai

Ministar gwamnatin Buhari Sadiya Farouq za ta bayyana a gaban EFCC.

Sabon hari ya yi ajalin babban limamin masallacin Jumu’a a yankin Bokkos a jihar Filato.

Gwamnonin Arewa Maso tsakiya sun kudiri aniyar hada karfi da karfe don dakile Kashe-Kashen da Ke afkuwa a yankin.

Hukumar ICPC ya gayyaci dan jaridar nan da ya fallasa yadda wata jami’a a kasar Jamhuriyar Benin ke bayar da shaidar kammala Digiri’ a kasa da wata biyu.

Sarkin Benin Uku Akpolokpolo, Ewuare II, ta bakin sakataren watsa labaransa, Osaigbovo Iguobaro ya yi karin haske kan ziyarar dan sarkin Kano zuwa coci.

Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo ya dakatar da dukkan ciyamomin kananan hukumomi da Kuma kansiloli 33 a fadin jihar.

Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutum 4 a wani hari da suka kai babban kantin Wisfom a Nasarawa.

Shugaban Hukumar Jiragen Kasa ta Najeriya ya sanar da dawowar daukar fasinja da dare daga Abuja zuwa Kaduna da ma sauran sassan kasar a cikin sabuwar shekarar nan.

Najeriya ta rufe jami’o’in Æ™asashen waje 18 bayan rahoton ‘digiri É—an Kwatano.

Hukumar Hisba ta ce ta kama wata motar dakon kaya makare kwalaben barasa fiye da 24,000 a Jihar Kano.

Allah ya karbi rayuwar Sheikh Usman Abubakar Damana a yau Laraba 3 ga watan Janairu a jihar Kebbi.

Tagwayen bama-bamai sun kashe fiye da mutum 100 a Iran.

An tuhumi tsohon Shugaban Saliyo Emest Koroma da yunƙurin juyin mulki.

Jirgin helikwafta na sojin Uganda ya rikito kan wani gida.

Morocco ta ƙwace tan 1.4 na hodar iblis da aka boye cikin ayaba.

Rasha ta harba makamai masu linzami fiye da 500 kan Ukraine.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *