Daga Baba Usman Gama
Gwamnatin tarayya za ta fito da wani tsarin don farfaÉ—o da darajar naira.
Majalisar Wakilai ta umarci gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN ya hallara a gabanta don yi bayani kan matakin ba da dala kan kayayyaki 43.
Majalisa ta kafa kwamatin bincke kan gyaran matatun fetur na Najeriya.
Gwamnan Katsina ya raba wa daliban Jihar miliyan 640 a matsayin tallafin karatu.
An yanke wa likitan da ya yi wa ’yar uwar matarsa fyade daurin rai da rai a Legas.
Gwamnonin APC na jihohin Kudu maso Yamma sun gana da gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo.
Majalisar jihar Benue ta bai wa gwamnan jihar wa’adin sa’o’i don kawo karshen rashin tsaro.
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Enugu ta bayyana kujerar ofishin sakataren jam’iyyar PDP na Æ™asa a matsayin wacce ba kowa a kanta.
Kungiyar ROTARY a Kano ta gudanar da gangamin yaki da cutar shan inna a jihar.
Mazauna Birnin Gwari sun ce kusan kullum sai ‘yan bindiga sun kai hari kauyuka ko kan titi.
Harin ‘yan bindiga a Mexico ya kashe mutane kusan 30.
Wata matashiya na iya rasa ranta saboda dukan ‘yan sandan tabbatar da da’a a Iran.
Macron ya gana da shugaban Falasɗinawa a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.
Hamas ta harba rokoki kan birnin Tel Aviv.
Amurka ta kawo ƙarshen agaji a Gabon sakamakon juyin mulki.
Mutane da dama sun mutu a hatsarin kwale-kwale a DR Congo.
An ci tarar Kano Pillars miliyan daya kan kutsen magoya baya cikin filin wasa.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/KpTjEvHUjd3CVzIQp8CSkZ