Daga Baba Usman Gama
Majalisar dokoki na son a daina yi wa mata masu juna biyu hukuncin kisa.
Sanata Ali Ndume ya shawarci Shugaba Tinubu ya saurari koken masu shirin zanga zanga kan tsadar rayuwa.
Gwamantin tarayya ta ce ba dai-dai bane matatar Dangote ta riƙa shigo da fetur ita kadai.
Sojoji sun ceto wata yar matan Chibok da’ya’ya 2 suniÆ™a ta ga Gwamnatin Borno.
Kotu a jihar Legas ta daure wani malami dake kula da daliban makarantar kwana a gidan yarin Kirikiri kan zargin yin lalata da dan shekara 12 da dubura.
Dangote zai sayo É—anyen man fetur daga Libya da Angola.
Jam’iyyun adawa sun gargaÉ—i gwamnatin Tinubu kan zanga-zanga.
Jami’ar Abuja ta janye yajin aikin kwanaki 82 da ta ke yi, ƙarƙashin Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU.
Gwamnatin Kano za ta gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi.
Wakilin ƙaramar Hukumar Gwale a majalisar Kano ya zargi magoya bayan Sarki Aminu da cin zarafinsa.
Mabiya Addinin Kirista Iklisiyyar United Methodist Church a Najeriya, sun gudanar da zanga zanga ta lumana don nuna kyama ga batun auren jinsi da wassu Shugabannin Iklisiyar Methodist Church ke kokarin ganin mabiyan sun amince dashi.
‘Yan Majalisar dokokin Amurka sun bukaci daraktar hukumar tsaron farin kaya tai Murabus
Zaftarewar ƙasa ta kashe aƙalla mutum 55 a Habasha.
Tsohuwar kakakin majalisar wakilan Amurka, Nancy Pelosi ta nuna goyon bayanta ga Kamala Harris a matsayin wadda za’a tsayar takarar shugabancin Amurka.
Firaministan Birtaniya ya yi kira da a yi gaggawar tsagaita wuta a Gaza.
Masu goyon bayan Falasɗinawa a Amurka sun yi zanga-zanga kan zuwan Netanyahu ƙasar.
PSG za ta yi kokarin kulla yarjejeniya da Man. United kan Sancho amma kuma tana son dauko Bruno Fernandes.
Tattaunawa tsakanin PSG da Napoli kan batun sayen Victor Osimhen, ta yi nisa.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj