Takaitattun Labaran Yammacin Na Ranar Laraba 11/08/1445AH – 21/02/2024CE

IMG 20240103 WA0021

Daga Baba Usman Gama

Shugaba Tinubu ya amince da naɗin Kemi Nanna Nandap a matsayin Kwanturola-Janar ta Hukumar Shige da Fice ta kasa.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce Gwamnatin Tarayya ta bai wa kowanne gwamna naira biliyan 30 domin rage wa talakawa raɗaɗin tsadar rayuwar da suke fuskanta.

Majalisar Dattawa ta yanke shawarar gudanar da bincike a kan yadda Gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi amfani da basukan naira tiriliyan 30 da ta karɓo daga CBN.

Majalisar dattawa ta yi watsi da cire tallafin lantarki.

Rundunar ƴan sandan Jigawa na bincike kan wata mata da aka yiwa yankan rago kuma aka raunata ƴarta mai shekaru 11 a birnin Dutse na Jigawa.

Kotu a Abuja ta bayar da umarnin wucin gadi na kwace Naira biliyan 1.58 da ake alakantawa da tsohon Manajan Bankin NIRSAL Aliyu Abatti Abdulhameed.

An tsaurara matakan saro a harabar Majalisar Dokokin Jihar Jigawa, wadda ake shirin tsige shugabanta.

EFCC ta tsare wasu ’yan kasuwa a samamen da jami’anta suka kai kasuwar ’yan canji ta WAPA da ke Jihar Kano ranar Laraba.

Jami’an tsaro sun kai samame da kama masu canjin kuɗi a birnin Ibadan na Jihar Oyo.

’Yan bindiga sun yi awon gaba da fasinjoji akalla 26 a wasu hare-hare guda biyu a kan hanyar Funtua zuwa Gusau.

Yakubu Gowon ya buƙaci Ecowas ta gaggauta ɗage wa Nijar takunkumai.

Jam’iyyar APC ta ayyana zaben fitar da gwani na gwamna a jihar Edo a matsayin wanda bai kammala ba.

Rahotanni sun ce aƙalla sojojin Rasha 60 ne suka mutu bayan da aka harba wani makami mai linzami kan wani wurin atisaye a gabashin Ukraine da aka mamaye.

An kama ƴan sandan Kenya kan zargin fataucin bil adama.

Majalisar Dokokin Ghana ta yi watsi da ƙudurin sassauta hukunci kan ƴan luwaɗi.

‘Yan kamaru na kokawa da matsalar hauhawar farashin kaya.

Gwamnatin Indiya ta nemi tattaunawa da fusatattun manoman kasar.

Kakakin majalisar Cuba na ziyara a Kenya kan makomar likitocin kasar da ke hannun Al-shabab.

Dan wasan Super Eagle Ahmed Musa ya kai wa Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ziyarar ban girma a yau Laraba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *