Daga Baba Usman Gama
Shugaba Tinubu ya ce yana sane da sadaukarwar da ‘yan kasa ke yi game da sauye-sauyen da gwamnatinsa take aiwatarwa tun bayan hawansa mulki.
NDLEA ta kama kwayoyin Tramadol sama da milyan 7 da kwalaben Kodin kusan dubu 100 a Legas.
Rundunar Æ´an sandan jihar Ogun ta fitar da sanarwa dangane da harbin da aka yi wa jarumin fina-finan Nollywood, Azeez Ijaduade.
Akwai ruÉ—ani game da ‘wasikar’ da Sheikh Dahiru Bauchi ya rubuta kan shari’ar zaÉ“en gwamnan Kano.
Diezani Alison-Madueke, tsohuwar ministar man fetur ta musanta cewa an yi wata hira da ita a Landan kwanan nan inda ta roƙi Shugaba Bola Tinubu da ya bar ta ta dawo gida.
An bankado yadda tsohon Gwamnan CBN Godwin Emefiele ya saye bankunan Union, Keystone da Polaris ta barauniyar hanya.
An dakatar da wasu dalibai 7 na kwalejin kimiyya ta Isah Mustapha Agwai da ke jihar Nasarawa kan yada hotunan rashin tarbiyya yayin bikin yaye dalibai.
An buƙaci gwamnatin tarayya da ta ƙwace wasu bankuna guda 2 da aka sayar a zamanin Godwin Emefiele a matsayin gwamnan CBN.
Aƙalla mutum 11 ne aka tabbatar da rasuwarsu bayan wani mummunan hatsarin mota da ya auku a garin Kwanar Gujungu da ke jihar Jigawa.
Wasu sababbin ’yan haya sun tsere da ’ya’ya 4 na makotansu kwana 3 da kama haya agidan da suke a Umu’ahiya fadar Jihar Abiya.
Beijing na fuskantar tsananin sanyi da zubar kankara.
Amurka ta ce ta daÆ™ile hari a Tekun Maliya daga ‘yan tawayen Houthi.
An kashe sojojin Isra’ila takwas a Gaza, an ji wa shida mummunan rauni.
Gwamnatin Burundi ta zargi kunfitar yan tawayen RED-Tabara da kashe akalla fararen hula 20.
Faransa ta cafke wasu mutane 5 da take zargi da kitsa ta’addanci a kasar.
Wasu yan takarar shugabancin kasar Congo sun yi watsi da sahihancin zaben shugancin kasar da aka gudanar.
EPL: Wolverhampton ta sami nasara akan Chelsea da ci 2:1 a wasan yau.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp