Tarin Zargin Ta’addancin Da DSS Kewa Tsohon Gwamnan CBN Emefiele


Wasu daga irin zarge zargen da goyon baya da ɗaukar nauyin ta’addanci da ake zargin Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele yayi  ko ya keyi.

Alfijir Labarai ta rawaito Jami’an DSS ne a baya su ka yi masa wannan zargi, har su ka yi ƙoƙarin kama shi.

DSS na zargin Godwin Emefiele da ɗaukar nauyin ta’addancin da ƙungiyar IPOB ke aikatawa.

Haka dai bayanan da jami’an tsaro su ka yi wa kotu su ka nuna. Waɗannan bayanai  jaidar Premium Times ta samesu.

IPOB dai Ƙungiyar Rajin Kafa Biafra ce, wadda a shekarun nan ta buɗe wuta sosai wajen kisan jami’an tsaro da banka wa gine-ginen hukumomin gwamnatin tarayya wuta. Musamman ofisoshin INEC da ofishin ‘yan sanda.

Tun cikin 2017 kotu ta ayyana cewa IPOB ƙungiyar ta’addanci ce.

A cikin Disamba, 2022 ne DSS su ka garzaya Babbar Kotun Tarayya neman a ba su sammacin kama Godwin Emefiele, saboda zargin ta’addancin da ake yi masa.

Biri Ya Yi Kama Da Mutum:

Yadda Kotu ta ƙi bawa DSS Sammacin Iznin Shaƙo Wuyansa.

Abin ɓoye ya fito fili, domin tabbatattun bayanai na nuna cewa a ranar 9 Ga Disamba, Hukumar DSS ta garzaya Babbar Kotun Tarayya, inda ta nemi a ba ta sammacin iznin kamo tsohon Gwamnan Bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele, amma kotun ta ƙi.

Shugaban Alƙalan Babbar Kotun Tarayya John Ɗantsoho ya ƙi amincewa da roƙon da DSS ɗin su ka yi, bisa ga dalilin cewa sun kasa bai wa kotu gamasasdun dalili ko hujjar kama Gwamnan Babban Bankin na CBN.

DSS dai sun shigar da ƙarar neman sammacin kama Emefiele a wasiƙar da su ka aika wa Babbar Kotun Tarayya, mai lamba FHC/ABJ/CS/2255/2022, wanda Ɗantsoho ya yi zama kan buƙatar a babbar kotun tarayya mai Lamba 7 Abuja.

Sai dai DSS sun bayyana cewa su na son su kama Emefiele “domin bincikar sa kan zargin ɗaukar nauyin ta’addanci, harƙalla, laifin karya tattalin arzikin ƙasa da kuma laifukan da su ka shafi muhimmin al’amarin tsaron ƙasa.”

Mai Shari’a Ɗantsoho ya ƙi amincewa, bisa dalilin cewa ba a fito takamaimai an bayyana laifukan da ya yi har ake zargin sa ba, Ma’ana, a cewar sa, DSS ta bai wa kotu ba’asi a ƙudundune.

“Sannan kuma DSS ba su bayyana shin wane Godwin Emefiele su ke neman a ba su sammacin kamawa ba, sun dai rubuta Godwin Emefiele kawai.

“To in dai Godwin Emefiele Gwamnan CBN su ke nufi, matsayin sa na mai riƙe da tasarifin kuɗin Najeriya, kama shi sai da sanin shugaba.”

Hakan dai na nufin ba zai yiwu a kama Emefiele ba sa sanin Shugaba Muhammadu Buhari ba kenan.

Emefiele dai ya bi Shugaba Muhammadu Buhari zuwa Amurka kwanaki biyu da kotun ta hana a damƙe shi.

Yayin da ya ke shan suka kan taƙaita adadin kuɗaɗen da za a iya cira ta ATM da POS zuwa naira 20,000 kacal, ana zargin sa cewa ya kasa yin komai dangane da faɗuwar darajar Naira, inda sai da ta kai har naira 740 a kssuwar ‘yan canji.

Haka kuma Da Majalisar Tarayya Gudaji Kazaure na zargin sa salwantar da naira tiriliyan 89 na harajin stamp duty.

A gefe ɗaya kuma, yau Talata ce Shugaba Buhari ya kulle ƙofa ya yi ganawar sirri da Gbajabiamila.

A ranar Talata ɗin ce Shugaba Muhammadu Buhari ya yi ganawar sirri tare da Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila.

Shugabannin biyu dai sun gana ne kan batun tsarin taƙaita cirar kuɗi zuwa naira 20,000 kacal a kullum da Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Goodwin Emefiele ya ƙirƙiro da amincewar Buhari.

Bayan ganawar ta su, Gbajabiamila ya shaida wa manema labarai na Fadar Shugaban Ƙasa cewa, “mun tattauna batun Gwamnan CBN Godwin Emefiele, da kuma batun zaɓen 2023, wanda mu ka tattauna batun hanyoyin kauce wa tashen-tashen hankula lokacin zaɓe. Mun kuma tattauna wasu batutuwa daban-daban.

Buhari da Gbajabiamila sun gana ne a ranar da Emefiele ya ƙi zuwa amsa gayyatar da Majalisar Tarayya ta yi masa, domin zuwa ya yi bayani kan tsarin taƙaita cirar kuɗi zuwa naira 20,000.

Dama kuma Majalisa ta umarce shi da ya dakatar da aiwatar da tsarin taƙaita cire kuɗaɗen.

Manema labarai sun tambayi Gbajabiamila dangane da zargin da Ɗan Majalisar Tarayya Gudaji Kazaure ke wa Gwamnan CBN cewa kuɗaɗen harajin stamp duty sun salwanta a hannun sa har naira tiriliyan 89, sai Gbajabiamila ya ce Gudaji shi kaɗai ke kiɗan sa, ya ke rawar sa, ba da yawun Majalisar Tarayya ya ke yi ba.

Emefiele: Abin Ɓoye Ya Fito Fili:

Makonni takwas bayan DSS sun nemi iznin kama Emefiele amma kotu ta hana su.

1. Ana zargin sa da yi wa Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari zagon-ƙasa.

2. Ana zargin sa da ɗaukar nauyin kashe wa kungiyar IPOB maƙudan kuɗaɗe ana aikata ta’addanci.

3. Ana zargin sa da aikata laifukan da su ka shafi zagon ƙasa ga tattalin arzikin Najeriya, laifuka masu kawo wa tsaron ƙasa cikas.

4. Ana zargin sa da kacalcala maƙudan kuɗaɗen Ayyukan Bunƙasa Harkokin Tallafa Wa Masu Ƙananan Sana’o’i, wato kuɗaɗen NISRAL.

5. Ana zargin Emefiele da facaka da kuɗaɗen Shirin Lamunin CBN na Anchor Borrowers’ Scheme.

A ranar 7 Ga Disamba, 2023 wasu lauyoyin DSS su huɗu su ka shigar da ƙarar Emefiele a Babbar Kotun Tarayya, a gaban Mai Shari’a John Tsoho.

Sun nemi tsare Emefiele har tsawon kwanaki 60 kafin su kammala binciken sa.

Wani jami’in DSS mai suna Umar Salihu ya kai wa Babbar Kotun Tarayya kwafen rantsuwar ‘affidavit’, mai ƙunshe da yadda su ka yi bincike dalla-dalla har su ka kai ga zargin laifukan da su ke cewa Emefiele ya aikata.

“Dalili kenan wannan hukumar tsaro ne neman iznin Babbar Kotun Tarayya ta ba ta sammacin kama Emefiele, ta tsare shi kwanaki 60 har sai ta kammala sauran bincike tukunna.” Inji kwafen ‘affidavit’ ɗin da DSS su ka gabatar wa kotu.

DSS sun zargi Emefiele ya riƙa bai wa IPOB kuɗaɗen da ya tara domin ya yi takarar zaɓen 2023 da kuma kuɗaɗen da ya riƙa kamfata ya na ɓoyewa daga asusun gwamnati.

Har yau Emefiele ko gwamnatin tarayya babu wanda ya yi magana kan wannan batu.

PREMIUM TIMES.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

2 Replies to “Tarin Zargin Ta’addancin Da DSS Kewa Tsohon Gwamnan CBN Emefiele

  1. Kuna kokari , amma arinka dubawa don gano kurakurai. Misali ‘ A ranar 7 ga watan Disemba 022 ( ba 2023 ba)lauyoyin Dss suka ……

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *