Tawagar, ƙarkashin jagorancin Mataimakin Shugaban Ƙasa Sanata Kashim Shettima ta miƙa saƙon ta’aziyyar shugaban ƙasar ga gwamnatin jihar Borno da al’ummar Gwoza, har ma Mataimakin shugaban ƙasar ya bayar da gudummawar kuɗaɗe ga waɗanda abin ya shafa da iyalan wadanda suka rasa rayúkañsu.
Alfijir labarai ta ruwaito a cewar Shettima, Zuciyar Shugaban Ƙasa na tare da iyalan mutane 32 da suka rása rayúkańsu a háriñ, da kuma wasu 42 suka jikkáta, haka ma sauran mutane 14 da aka sallama daga asibiti.
Shugaban ya lashi takobin kawo ƙarshen ta’addáńci a Najeriya da kuma sauke nauyin kare ráyúka da dukiyoyin ‘yan ƙasar kamar yadda ya ɗauki alkawari.



Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj