Tinubu Ya Bayyana Lokacin Da Za’a Saurari Sunayen Ministoci Kashi Na Biyu

Sauran sunayen, ba a tabbatar da adadin su nawa ne ba, mai yiwuwa kimanin 12, watakila 13, za a mika wa majalisar a kwanaki masu zuwa.

Alfijir Labarai ta rawaito shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, ya bayyana ranar Alhamis a Abuja.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya bayyana cewa Gbajabiamila ne ya mika jerin sunayen ministocin ga majalisar dokokin kasar kuma shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ya karanta.

Gbajabiamila ya bayyana cewar za a aika kashi na biyu mai kunshe da sunaye 13 ga majalisar, inda ya ce hakan na daga cikin tsarin samar da majalisar ministocin gwamnati.

‘’Kamar yadda kuka sani yana da kwanaki 60 daga lokacin rantsar da shi, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

Ya cika wannan bukata ta kundin tsarin mulki ta hanyar gabatar da sunaye 28 a yau.

‘’Kamar yadda wasikar tasa ta bayyana, kuma aka karanta a zauren majalisar dattawa, sauran sunayen, ba a tabbatar da adadin su nawa ne ba, mai yiwuwa kimanin 12, watakila 13, za a mika wa majalisar a kwanaki masu zuwa.

“Game da wadanda aka nada su kansu, kuma kamar yadda na fada, Shugaban kasar ya dauki lokacinsa wajen tantance wadannan sunayen,” in ji shi.

Shugaban ma’aikatan ya ce shugaban ya yanke shawarar jan layi ne ta hanyar kin sanya sunayen wadanda aka nada a cikin wasikar ga majalisar dattawa domin ba da damar tantancewa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *