Tirka-Tirka! An cafke ƴar bautar ƙasa ta bogi a jihar Nassarawa

FB IMG 1709394930999

Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta kama wata ƴar bautar ƙasa ta bogi mai suna Ogeh Bethel Chibuife bisa laifin shiga sansanin horaswa na Magaji Dan Yumusa da ke Keffi, babban birnin jihar ba bisa ka’ida ba.

Alfijir labarai ta rawaito hakan na kunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ƴansandan Ramhan Nansel ya fitar, inda ya ce wadda ake zargin ta zo ne daga jami’ar jihar Ebonyi.

Nansel ya ce wadda ake zargin, wanda daliɓar ƙarin shekara ne daga Jami’ar Jihar Ebonyi, ta sulale ta shiga sansanin horaswa na NYSC wanda ake ɗaukar kwanaki 21 ana yi, da nufin samun horo a rukunin A, kashi na farko na 2024, inda daga bisani aka gano ta.

Ya ce wani jami’in NYSC ne ya kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda a ranar Lahadi, kuma jami’an rundunar ne suka kama ta.

“Ta faɗa cewa a shekarar 2022 ya kamata ta kammala karatunta, ammasai ta faɗi wasu kwasa-kwasa, kuma a ƙoƙarinta na ɓoye karyar da ta yi wa iyayenta, ta je kasuwa ta siyo rigar kayan bautar ƙasa. Bayan ta sulale ta shiga cikin sansanin don ɗaukar hotuna ta aika wa iyayenta kafin aka kama ta,” in ji shi.

BBC

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *