Tirka-Tirka! NNPP Za Ta Binciki Kwankwaso Da Wasu Kan Zargin Karkatar Da Biliyan 1 N1b


Tsagin jam’iyyar NNPP karkashin jagorancin Manjo Agbo ya bayyana cewa za su binciki dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Sanata Rabi’u Kwankwaso da wasu daga cikin magoya bayansa bisa zargin karkatar da sama da Naira biliyan daya da aka samu daga kudaden sayan fom din takara

Alfijir Labarai ta rawaito hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da tsagin suka zargi wani jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima da fifita wasu ‘yan takarar jam’iyyar akan sauran ‘yan takara.

Jam’iyyar ta NNPP yayi wannan zargin ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadin da ta gabata ta hannun sakataren yada labaran jam’iyyar NNPP, Abdulsalam Abdulrasaq, bayan wani taro a sakatariyarsu dake Abuja.

Ya ce, “NNPP za ta gudanar da cikakken bincike a kan almundahanar sama da Naira biliyan daya da aka samu daga sayar da fom ga masu neman takara a jam’iyyar daga watan Maris na 2022 zuwa yau. Taron ya yanke shawarar gayyatar hukumomin tsaro da abin ya shafa domin su binciki asusun jam’iyyar yadda ya kamata da nufin neman bayanai daga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, da shugaban jam’iyyar da ya fice a watan Maris na 2023, da korarren shugaban riko, da kuma sakataren jam’iyyar na kasa.

“Za’a yi wannan ne don dawo da kwarin gwiwar ‘yan jam’iyyar da ‘yan takarar da suka fitar da kudaden da suka tara don sayen fom. Jam’iyyar ta kuma nemi dalilin da ya sa dakin kula da zabe aka Maida shi gidan dan takarar shugaban kasar.

Abdulrasaq ya tabbatar da cewa jam’iyyar ta janye daga yarjejeniyar fahimtar juna da ta rattabawa hannu a baya da kungiyar Kwankwasiyya da National Movement, inda ya dage cewa manufofin kungiyoyin biyu suna farantawa mai su ne kawai ba jam’iyyar ba y.

Ya kuma yi alkawarin bincikar dalilin da ya sa jam’iyyar ta fifita Kwankwaso da kuma zargin hana wasu masu neman tikitin takara kujera daya.

“Jam’iyyar ta kuma kuduri aniyar neman dalilin da ya sa aka hana wasu ‘yan takarar shugaban kasa ‘yancin sayen fom da shiga zaben fidda gwanin da ya samar da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ba bisa ka’ida ba tare da jaddada cewa hakan ya saba wa adalci da doka wanda babbar jam’iyyarmu take fatan tabbatarwa .

Jam’iyyar ta yi kira ga dimbin ‘ya’yanta da magoya bayanta da su kwantar da hankalinsu dangane da wannan mugun nufi na tafiyar Kwankwasiyya da aka yi wa ’ya’yanta bisa kuskure cewa an sayar musu da jam’iyyar tare da yin kira ga duk wadanda suka fice daga jam’iyyar Saboda wancan dalili. Inda yace jam’iyyar ta yanke shawarar yin garambawul ga tsarinta a dukkan matakai a fadin kasar nan cikin makonni masu zuwa,” inji shi.

Da yake mayar da martani, Audita na kasa na NNPP, Ladipo Johnson ya wanke Kwankwaso daga aikata wani laifi, inda ya ce duk zarge-zargen da ake yi masa ba gaskiya bane kuma basu da tushe ballantana makama.

Johnson ya kuma yi mamakin dalilin da ya sa ba a taso da zargin ba har sai da aka kori shugabannin bangarorin daga jam’iyyar.

“Shin Kwankwaso yana sayar da fom ne? Shi ba dan jami’in jam’iyya ba ne, ko kuma jami’in kula da asusu ne? Me yasa kuke daukar su da mahimmanci? Ya kamata a bayyane ga dukan duniya abin da waɗannan mutane suke ƙoƙarin yi. Tuni fa jam’iyyar ta kore su.

“Me ya sa ba su yi wannan zargin ba kafin zabe, da lokacin da kuma nan da nan bayan zaben? Me ya sa suke fadin wadannan kalamai bayan an kore su daga jam’iyyar?” Ya tambaya.

The Punch

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@musa_bestseller

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *