Tirkashi! Ecowas ta tabbatar da dakatar da Nijar daga ƙungiyar

FB IMG 1702593546086

Ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirka ta Yamma, Ecowas ta ce ta dakatar da Jamhuriyar Nijar daga dukkan harkokin ƙungiyar ƙasashen har sai ta mayar da mulkin dimokraɗiyya.

Alfijir labarai ta rawaito matakin na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Ecowas ta fitar da yammacin Alhamis, inda ta ce daga ranar 10 ga watan Disamba, ƙungiyar ƙasashen ta yarda cewa ba shakka, sojoji sun yi wa Shugaba Bazoum Mohamed juyin mulki.

Ta ce kafin wannan lokaci, ƙungiyar na ɗaukar abin da ya faru a Nijar daga watan Yuli, a matsayin yunƙurin juyin mulki don haka, ba a dakatar da Nijar daga shiga harkokin mulki na Ecowas ba, abin da ke nufin jami’an gwamnatin Bazoum za su iya wakiltar Nijar a tarukan Ecowas.

Ecowas ta ƙara da cewa har zuwa ranar da ta yi taronta na Abuja tsakanin shugabannin ƙungiyar ƙasashen, wanda shi ne karo na 64, Ecowas na ɗaukar Mohamed Bazoum a matsayin shugaban jamhuriyar Nijar.

Sanarwar mai yiwuwa na martani ne ga wasu kalamai da jami’an gwamnatin mulkin sojan Nijar da suka hamɓarar da Bazoum Mohamed suka yi a ranar Laraba, suna zargin Ecowas da barin jami’an gwamnatin Bazoum na halartar tarukan ƙungiyar da sunan Nijar, Abin da suka ce ya ci karo da doka.

BBC

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *