Kungiyar Kwadago ta Najeriya, NLC ta sanar da janye zanga-zangar neman saukin tsadar rayuwa a ranar ta biyu wato ranar Laraba.
Alfijir labarai ta rawaito Kungiyar ta ce ta dage zanga-zangar ne ta ranar Laraba ne saboda ta sake bai wa gwamnati karin makonni biyu har zuwa 13 ga watan Maris domin biyan bukatunta.
A ranar Talata ranar farko ta zanga-zangar, daruruwan masu zanga-zangar neman saukin matsin rayuwa da ake ciki a Najeriya ne suka fantsama kan titunan biranen kasar bisa umarnin kungiyar ta kwadago.
Kungiyar kwadago dai ta yi kira da a yi zanga-zangar gargadi ta kwana biyu. To sai dai yanzu kungiyar ta sanar da janye zanga-zangar ta rana ta biyu wato ranar Laraba 28 ga watan Fabrairu.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V