Tsalle Daya! An Cafke Wasu Malamin  Bogi A Jami’ar Bayero dake Kano.

IMG 20240726 WA0556

Daga Aminu Bala Madobi

Jami’an tsaro dake aiki a Jami’ar Bayero dake jihar Kano, sun samu nasarar cafke wasu mutane biyu wadanda suke gabatar da kansu a matsayin malamai dake koyarwa a Jami’ar.

Alfijir labarai ta ruwaito rahotanni sun ce malaman bogin da suka hada da David Iluebe, dan jihar Edo, da kuma Chike E. Eke, dan jihar Delta,  ana dai tuhumar su da laifin shiga cikin aji a tsangayar koyar da ilimin injiniyarin, tare da gabatar da kansu a matsayin malaman sashen.

A wata sanarwa da jami’in yada labarai na ofishin Rijistaran Jami’ar Bala Abdullahi, ya rabawa manema labarai, sanarwar ta ce, malaman bogin sun gabatar da kwafin wasu littattafai guda hudu don sayar wa dalibai.

Malaman bogin na yin barazana ne ga dalibai ‘yan ajin farko cewa tilas ya zama wajibi sai sun sayi littattafan, inba haka su fadi warwas a jarabawar gwaji wato test.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *