Daga Aminu Bala Madobi
Jami’an tsaro dake aiki a Jami’ar Bayero dake jihar Kano, sun samu nasarar cafke wasu mutane biyu wadanda suke gabatar da kansu a matsayin malamai dake koyarwa a Jami’ar.
Alfijir labarai ta ruwaito rahotanni sun ce malaman bogin da suka hada da David Iluebe, dan jihar Edo, da kuma Chike E. Eke, dan jihar Delta, ana dai tuhumar su da laifin shiga cikin aji a tsangayar koyar da ilimin injiniyarin, tare da gabatar da kansu a matsayin malaman sashen.
A wata sanarwa da jami’in yada labarai na ofishin Rijistaran Jami’ar Bala Abdullahi, ya rabawa manema labarai, sanarwar ta ce, malaman bogin sun gabatar da kwafin wasu littattafai guda hudu don sayar wa dalibai.
Malaman bogin na yin barazana ne ga dalibai ‘yan ajin farko cewa tilas ya zama wajibi sai sun sayi littattafan, inba haka su fadi warwas a jarabawar gwaji wato test.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj