Tsaro! An sami nasarar  kama wasu bama-bamai 399 da tarin miyagun ƙwayoyi a Najeriya

Mayaƙan waɗanda akasari kan auka wa mutane a kan babura, sun yi ƙaurin suna wajen kashe-kashe da jikkata fararen hula, da satar mutane ciki har da mata da ɗalibai ‘yan makaranta,

Alfijir Labarai ta rawaito Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya, NDLEA sun ce sun kama bama-bamai kimanin 399 daga hannun wani mutum a kan hanyar Mokwa-Jebba a ranar 7 ga watan Satumba.

Hukumar ta ce ta damƙa mutumin da ake zargi mai shekara 39 ga hukumomin soji a jihar da abin ya faru wato Neja.

Ya dai bayyana cewa an miƙa masa bama-baman ne a wani dandali da ke cikin birnin Ibadan, domin kai wa wani mutum a jihar Kaduna.

Zuwa yanzu babu masaniya a kan abin da za a yi da bama-bamai masu tarin yawa haka da mutumin ya yi safara zuwa arewacin Najeriya.

Bama-baman dai irin waɗanda ake haɗawa a gida ne, da aka fi sani da suna abubuwa masu fashewa.

Jihar Kaduna da maƙwabtanta irinsu Neja da Zamfara da Katsina, suna fama da mummunan rikicin ‘yan fashin daji masu kai hare-hare da bindigogi a kan ƙauyuka da garuruwa.

Mayaƙan waɗanda akasari kan auka wa mutane a kan babura, sun yi ƙaurin suna wajen kashe-kashe da jikkata fararen hula, da satar mutane ciki har da mata da ɗalibai ‘yan makaranta, inda suke tsare su har sai an biya kuɗin fansa.

A watan Maris ɗin 2022, hukumomi sun zargi ‘yan fashin dajin da haɗa kai da mayaƙan ƙungiyar Boko Haram – ta ‘yan ta-da-ƙayar-baya musamman a arewa maso gabas – da ƙaddamar da hari kan jirgin ƙasan da ke cikin gudu a hanyarsa ta Abuja zuwa Kaduna.

Maharan sun yi amfani da bama-bamai wajen tarwatsa wani sashe na titin jirgin ƙasa da taragwansa, don tilasta wa jirgin tsayawa tare da sace gomman fasinjoji, bayan sun kashe wasu tare da raunata wasu da dama.

A baya-bayan nan ma, wani rahoto da aka kwarmata a kafofin yaɗa labarai, ya ambato hukumar tsaron farin kaya ta DSS na gargaɗin hukumomi da cewa wasu mutane ne kitsa makamancin harin da aka kai a kan jirgin ƙasa.

Sai dai, baya ga hare-haren ‘yan fashin daji, jihar Kaduna ta yi ƙaurin suna kan rikicin ƙabilanci da na addini da ma rikicin manoma da makiyaya.


Mai magana da yawun hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi ya shaida wa BBC cewa jami’an hukumar sun kuma kama wata mata mai shekara 60 da tabar wiwi mai nauyin kilogram 17 tare da wani mutum mai shekara 40, wanda shi ma aka cafke shi da jakunan tabar wiwi mai nauyin kilogram 261 a jihar Edo.

Jami’an hukumar ta NDLEA sun kuma lalata gonakin tabar wiwi mai fadin kadada 4.236347 a dajin Ekudo da ke karamar hukumar Onwude na jihar Edo.

An kama wani kaso na tabar wiwi da aka boye a cikin gwangwanin tumatir mai nauyin kilogram 20 da kwayar methamphetamine mai nauyin kilogram 1.6 da aka boye a cikin tufafi domin a fitar da su zuwa Dubai.

Jami’an hukumar sun yi wannan kamen ne a filin jirgin saman a Murtala Mohammed da ke Lagos kamar yadda Mista Babafemi ya bayyana:

“ Abin da ya faru shi ne a makon daya gabata a ranar Juma’a 8 ga watan Satumba ma’aikatan mu a filin jirgin saman na Murtala Mohammed da ke Lagos sun kama gwangwanin tumatir masu yawa,”

“Bayan amfani da naurar bincike sai mu ka gano cewa miyagun kwayoyi ne ake son yin safararsu zuwa Dubai. Hakan ya faru da wasu mutane da ke Lagos a wani kamfani inda aka gano irin wadanan kwayoyi boye a cikin tufafi da su ma aka so yin safararsu zuwa Dubai”, in ji shi.

Hukumar ta kuma ce ta kama wani matashi mai shekara 22 da tabar wiwi mai nauyin kilo gram 77.400 a ranar 7 ga watan satumba a kan hanyar Okene-Lokoja-Abuja kuma ta sake cafke kwayar Opiod a kan wannan hanya a ranar 4 ga watan Satumba kuma daga bisani ta kama wanda ake zargi da safararsu a jihar Gombe

Ta kuma ce ta yi wasu kame a jihohin Kano da kaduna wadanda su ma ake tuhuma da safarar miyagun kwayoyi.

BBC

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@musa_bestseller

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

One Reply to “Tsaro! An sami nasarar  kama wasu bama-bamai 399 da tarin miyagun ƙwayoyi a Najeriya”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *