Tsohon shugaban ƙasa , Olusegun Obasanjo ya ce wadanda suke cin gajiyar shigo da tataccen mai cikin Nijeriya ne ke kokarin yi wa matatar man Dangote zangon ƙasa.
Alfijir labarai ta ruwaito Obasanjo ya bayyana haka ne a wata hira da jaridar Financial Times.
Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaban Rukunin Kamfanunuwan Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya yi zargin cewa wasu ƴan Mafiya a harkar man fetur na kokarin kawo cikas ga matatar sa ta Dala Biliyan 20.
Amma a cewar tsohon shugaban, ya kamata matatar man ta amfani ƴan Najeriya da wadanda ba ƴan Najeriya ba.
“Kamata ya yi matatar man Aliko Dangote, idan ta kafu, to yan Najeriya da wadanda ba ‘yan Najeriya ba su sa hannun jari a Najeriya.
” Idan masu shigo da tataccen mai zuwa Nijeriya su ka ga cewa za a kashe musu kasuwa, to dole za su yi iya kokarin su su yi wa matatar man Dangote zangon ƙasa ,” Inji Obasanjo.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj