Matsayin Najeriya mai mafi yawan ɓaƙar fata a duniya, ƙasar na fama da wani “kamun-kazar-kuku” da gungun ‘yan siyasa da suka yi wa fannin shari’a.
Alfijir Labarai ta rawaito tsohon Shugaban Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA), Olumide Akpata, ya ce duk inda ka ga an samu mai shari’a nagari a ƙasar nan, to dace ne kawai, amma shi ma ɗin ba ta hanyar da ta dace aka naɗa shi ba.
Akpata ya ce tsarin da ake bi ana naɗa masu shari’a a Najeriya, a lalace ya ke, dalili kenan martabar fannin shari’a ba shi da wata daraja yanzu a Najeriya.
Tsohon Shugaban na NBA, ya bayyana haka lokacin da ya ke jawabi wurin Taron Ƙungiyar Lauyoyi ta Duniya, a Paris, babban birnin Faransa.
Da ya ke jawabi a gaban mahalarta taron, Akpata ya ce matsayin Najeriya mai mafi yawan ɓaƙar fata a duniya, ƙasar na fama da wani “kamun-kazar-kuku” da gungun ‘yan siyasa da suka yi wa fannin shari’a.
Ba shi kadai ya yi irin wannan kukan ba, shi ma farfesan shari’a, kuma tsohon Shugaban Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan Adam (NHRC), Chidi Odinkalu ya watsa wannan bayani a shafin sa na Tiwita a ranar Juma’a.
An nuno Akpata a cikin wasu gajerun faifan bidiyo biyu ya na nuna damuwa kan yadda masu mulki suka ƙudundune fannin shari’a, su ka cusa aljifan su.
Olumide wanda ya yi Shugaban NBA daga 2021 zuwa 2022, ya bayyana yadda tsarin naɗa alƙalai ya lalace a Najeriya.

“Inda duk ka ga an naɗa alƙali nagari, to sa’a ce kawai aka yi, amma ba bisa cancanta aka zaɓe shi ba, saboda tsarin da ake bi ana naɗa alƙalai gurɓattacce ne.”
A matsayin Akpata lokacin da ya ke Shugaban NBA, ya na cikin Majalisar Kula da Alƙalai ta Ƙasa (NJC). Wannan majalisa ce ke naɗa masu shari’a a manyan kotunan Najeriya. Kuma ita ce ke ladaftar da alƙalan da aka kama da laifi.
Domin Kallon Shirin FATAKE Mai Dogon Zango Season 1 Da Kuma CIgaba Da Kallon Season 2, Danna wannan Link din👇
https://youtube.com/@ukentertainmentkano?si=PPtuxJz76OuNP_oI
“Lokacin da ina Shugaban NBA, na gano yadda masu mulki ke ƙudundune fannin shari’a, su na jefawa aljifan su. Hakan ya lalata tasirin shari’a sosai a ƙasar nan. Kuma su dai kam su na cin ƙazamar riba da irin wannan tsiyar da suke tsulawa.”
Irin haka tasa Odinkalu ya fito ya yi taratsi kan naɗa wasu alƙalai, irin su Babban Jojin Najeriya, Olukayode Ariwoola da Shugaban Kotun Ɗaukaka Ƙara da sauran su.
Ya soki naɗe-naɗen da suka yi wa ‘ya’yan su da matan su a matsayin alƙalai. Da yawan ‘ya’yan wasu alƙalan da suka yi ritaya da waɗanda ke kan aiki, su ma an naɗa su alƙalai a ƙasar nan.
Akpata ya koka kan yadda gwamnoni ke yadda suka ga dama da alƙalan jihohi, ta hanyar hana su haƙƙin su da dokar ƙasa ta wajabta a yi masu.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp