Wani Magidanci Ya Hallaka Matarsa Da Dutsen Guga A Jihar Kano

📸Alfijir Labarai

Kotun majistre mai lamba 26 ta aike da wani magidanci Adamu Ibrahim gidan yari bisa zarginsa da hallaka matarsa ta hanyar buga mata dutsen guga a fuska.

Alfijir Labarai ta ruwaito lamarin ya faru ne a garin Kwanar Dangora da ke karamar hukumar Kiru a Jihar Kano.

Adamu ya bayyana cewar sabani ne ya shiga tsakaninsa da matarsa dalilin wata mata da ta nuna ba ta son mu’amalarsa da ita.

Sai dai ya ce ya yi ƙoƙarin fahimtar da ita, amma abin ya ci tura, inda ta ce babu ita babu zama da kishiya.

Daga nan ne a cewarsa ta kama shi da kokawa, kuma duk da ihun da yake yi ta ki rabuwa da shi, har ya aikata abinda ya aikata

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *