Ana Zargin Wani Malami Ya Dirkawa Dalibarsa ciki! Kuma Ya Tsere da Dalibar Mai Shekaru 16.
Best Seller Channel
Best Seller Channel
Best seller channel ta rawaito, mahaifin wata daliba mai suna Mista Stanley Ejekwu, ya zargi wani malami mai suna Caleb da yi wa diyarsa ciki tare da tserewa da ita.
Ekekwu ya yi zargin cewa watakila malamin ‘yarsa da ke unguwar Diobu a Fatakwal ya arce da yarinyar ne sakamakon cikin da ta ke dauke da shine, ya kuma roki jama’a da su taimaka masa wajrn ya bayyana inda ya boye ta.
Jaridar Punch ta bayyana Mahaifin yarinyar lokacin da yake zantawa da manema labarai a garin Fatakwal, ya ce ya ga wani mutum tare da ‘yarsa matashiya a wata hira ta WhatsApp inda wanda ake zargin ke tambayar yarinyar yaushe za su hadu don yin lalata, kasancewar sun shafe kusan watanni shida suna soyayya.
Best Seller Channel
Ejekwu ya bayyana cewa, ya buga wa mutumin waya tare da gargade shi da ya kauce wa yarinyar, ba tare da sanin shi malaminta ne ba.
Mahaifin ya ce yarinyar ta bar gidan ne a watan Disambar 2021 bayan an gano cewa tana da ciki.
Ya ce an kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda na Mile 3, yake bayyana mu su cewar, ina zargin malamin ya yi wa ‘yata ciki kuma ina zarginsa da bacewar ‘ta. “Me ya sa ‘yata ba za ta iya tuntuɓar kowa a gidana ba amma malamin ya tura mini lambar ɗiyata. Inji Mahaifin.
Best Seller Channel
Na yi imani yana rike da ‘yata ‘yar shekara 16. “Sauran daliban makarantar sun gaya mini cewa abincin da ’yata ta ke zuwa da shi makaranta, ita da wannan malamin suke ci tare a kullum.
“Don haka, na je ofishin ‘yan sanda na Mile 3 saboda na gano cewa ‘yata na da juna biyu kuma ta gudu daga gidan.
Na ga sakon soyayya da mutumin nan ya aiko mata sai na kira na gargadi shi kan abin da yake yi.
Daga baya, na gano tana da ciki. Na tambaye ta wanene ya yi mata ciki; sai ta fice daga gidan.
Best Seller Channel
Na kira mamallakin makarantar ne na sanar da cewa ‘yata ta bace tun watan da ya gabata, kuma ni kadai nake zargin wani malami ne a makarantarsu.
Daga baya sai mai makarantar ya kira ni ya tabbatar da cewa sun yi magana.
Hakan ya sa na je ofishin ‘yan sanda domin su taimake ni don nemo ‘yata,” in ji shi.
Malamin, a wani sakon murya da wakilinmu ya samu, ya musanta zargin da ake masa, ya kara da cewat ban san in da yarinyar take ba.
Na ji wannan batu ne lokacin da Mista Ekekwu ya zo makarantar ya ba da rahoton cewa ‘yarsa na da ciki kuma ta bace.
Best Seller Channel
Amma ban san komai game da hakan ba,” in ji shi.
Jami’an hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Grace Iringe-Koko, ta ce za yi mana cikakken bayanin halin da ake cikin idan an kammala bincike daga ofishin ‘yan sanda na Mile 3,.
Amma har zuwa yanzu lokacin hada wannan rahoto bata ce komai ba.