Wani Mummunan Hadari Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutane 2 Wasu 12 Sun Jikkata

Alfijr ta rawaito Hukumar kiyaye haddura ta tarayya reshen jihar Kogi ta ce wani hatsarin mota ya lashe rayukan mutane biyu, yayin da wasu 12 suka jikkata a ranar Lahadi a jihar.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa, hadarin daya tilo ya hada da wata motar bas kirar Toyota Hiace dauke da mutane 18 ciki har da direban.

Kwamandan hukumar na jihar Stephen Dawulung ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:30 na safe a kauyen Irepeni da ke kan titin Zariagi-Okene

Dawulung ya bayyana cewa hatsarin ya faru ne sakamakon gudu da kuma tashin taya da ya sa motar ta yi rani.

“Tuni jami’an mu da suka gudanar da aikin ceto, an Garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibitin Kekere dake mahadar Kabba, Zariagi.

“Tuni, gawarwakin fasinjojin da suka mutu an sallace su sanna an binne su, bisa amincewar yan uwansu,” in ji shi.

Kwamandan ya jajanta wa iyalan wadanda abin ya shafa, sannan ya bukaci direbobi su guji tafiye-tafiye da daddare, da saurin gudu da kuma amfani da tayoyin da suka lashe ko kuma wa adinsu ya kare.

Ya kuma umarci masu ababen hawa da su rika huta na mintuna 40 a duk lokacin da suke tuka motar sa’o’i hudu, don kawar da gajiya da bacci.

Dawulung ya godewa rundunar sojin bisa tallafin tsaro da suka baiwa jami’an FRSC da suka gudanar da aikin ceto.

Ya bukaci karin hadin kai da dukkan jami’an tsaro ‘yan uwa domin ceton rayuka da dukiyoyi a kan manyan tituna.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *