Wani Mummunan Hadari Yayi Sanadiyyar Konewar Fadawan Shehun Borno Su 3

Alfijr ta rawaito Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) ta tabbatar da afkawar wani hatsarin mota da ya rutsa da wasu fadawan Shehun Borno Alhaji Abubakar Umar Ibn Garbai El-kenmi su uku, a kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

Kwamandan Hukumar a jihar ta Borno, Utten Iki Boyi, ya shaida wa Jaridar Daily Trust a Maiduguri da safiyar ranar Talata.

Ya bayyana cewa mutane shida ne suka yi hatsarin wanda ya afku a ranar Litinin, amma an ceto uku, inda aka kai su wani asibiti da ke kusa da in da lamarin ya faru, a kusa da yankin Benisheik lokacin da motar ta yi dungure sannan ta kama da wuta.

Boyi ya ce nan da nan suka tura jami’an su zuwa wajen da lamarin ya faru, inda aka samu mutum uku sun ƙone kurmus har ba a iya gane su.

An samu nasarar ceto mutum uku inda aka kai su zuwa babban asibitin Beneshiek don yi musu magani. In Ji shi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Best seller Channel
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *