Wani Mummunan Hadari Yayi Sanadiyyar Rasuwar Mutum 5, Wasu kuma suka jikkata a wata babbar mota kirar Bus
Best Seller Channel
Best Seller Channel
Best seller channel ta rawaito, Mutane 5 ne suka mutu a wani hatsarin mota da ya afku a kauyen Zalanga dake kan hanyar Bauchi zuwa Darazo a karamar hukumar Darazo ta jihar Bauchi.
An bayar da rahoton cewa wasu biyar sun samu raunuka daban-daban.
Kwamandan hukumar kiyaye haddura ta kasa reshen jihar Bauchi Yusuf Abdullahi, wanda ya tabbatar wa da wakilin jaridar The Punch faruwar lamarin a ranar Litinin, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 10 na daren ranar Lahadi, hatsarin ya afku ne sa’o’i 24 bayan da mutane takwas suka mutu a wani mummunan hatsarin da ya afku a daren ranar Asabar da ta gabata, a kauyen Goltukurwa, Titin Dass-Bauchi.
Best Seller Channel
Hakazalika, a ranar Lahadin da ta gabata, an samu hadaruka da dama sun halaka mutane 20 a kauyen Bambal da ke kan hanyar Kano zuwa Jama’are da kuma kauyen Duhuwar Kura da ke kan hanyar Azare zuwa Zaki.
Da yake tabbatar da afkuwar hatsarin na baya-bayan nan, kwamandan sashin ya ce, sai da jami’an hukumar FRSC suka kwashe mintuna 39 kafin su isa wurin domin gudanar da aikin ceto.
Abdullahi ya bayyana cewa hatsarin ya rutsa da wata motar bas ta Volkswagen Sharon ta kungiyar ma’aikatan sufuri ta kasa da wani Isa Mohammed ya tuka motar da wata tirela.
Ya ce, “Abin takaicin ya faru ne a daren jiya da karfe 10 na dare a kauyen Zalanga da ke kan hanyar Bauchi zuwa Darazo.
Hadarin ya hada da motoci guda biyu. Hakan ya faru ne sakamakon lalacewa da tirelar ta yi a kan hanyar, in da Bas din ta shiga ciki wannan babbar motar.
Best Seller Channel
“Lokacin da aka kira mu, sai mutanenmu suka garzaya wurin cikin mintuna 39, suka garzaya da wadanda lamarin ya rutsa da su zuwa babban asibitin Darazo domin samun kulawa da kuma tabbatar da lafiyarsu.
“A asibitin ne wani likita ya tabbatar da mutuwar mutane biyar, wasu biyar kuma sun samu raunuka daban-daban.”