Alfijr ta rawaito ƴan bindiga da suka tilasta aiwatar da dokar zama a gida a jihar Imo sun kashe Yarima Iheme, kane ga Osita Iheme, jarumin da aka fi sani da Pawpaw.
The Punch ta wallafa shaidun gani da ido na cewa ‘yan bindigar sun yi tafiya ne a cikin motoci daban-daban, yayin da suke harbe-harbe ba kakkautawa a sassa daban-daban na jihar.
An kashe Prince ne a karamar hukumar Mbaitoli ta jihar yayin da suke tafiya tare da Martins Eke, kwamishinan ma’adanai na jihar.
An gano cewa ‘yan biyun na tafiya ne a cikin mota daya lokacin da ‘yan bindiga suka far musu, harin da ya wani dan sanda wanda shima ya rigamu gidan gaskiya.
Wani ganau, wanda ya yi magana da kafar yada labarai, ya yi ikirarin cewa harin na da nasaba da siyasa.
“Wannan harin yana da nasaba da siyasa. Mun gama a wani filin yakin neman zabe kuma muna kan hanyar zuwa Ubommiri.
An kai wa ayarin motocinmu hari ne a Amawuihe kafin Ubommiri,” inji ganau din.
“Kwamishinan da aka rantsar makonni biyu da suka wuce, ya sami munanan raunuka an garzaya da shi asibiti.
Maharan sun same sune a cikin wata mota kirar SUV ta Ford.
An ce wani bangare na kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB), ne ya ayyana dokar zaman gida na kwanaki biyar.
Umarnin wanda ya fara aiki a ranar Juma’a, zai ci gaba har zuwa ranar 14 ga watan Disamba.
Micheal Abattam, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, bamu samu jin ta bakinsa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
[07/12, 11:35 pm] Musa Best Seller: Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇