Alfijr ta rawaito wasu jajirtattun iyaye wato Hajiya Hauwa da Hajiya Sa adatu sun yi kira ga al’ummar Kano da kasa baki daya kan su zaɓi Peter Obi da Datti domin kawo sauyi cikin ƙasar nan baki daya.

Hakan na zuwa ne a wani Gangamin bayyana irin manufofin da ƴan takararsu ke da su kan al umma Kasar nan, biyo bayan halin kaka na kayi da jam iyyar APC suka saka ƙasar nan a ciki.
Haj Hauwa ta kara da cewar kun ga yadda zaben namun ya kasance bai haifar mana da daya mai ido daya ba, don haka muke tabbatarwa da al’ummar ƙasar nan yan takararmu sun shirya share muku hawaye da yardar Allah.

Lebour Party ta zaɓo muku da matasan yan takara masu jini a jika domin fitar da ku daga cikin wannan masifar da aka kaka ba mana cikin yardar Allah. In Ji Haj Sa adatu
A ƙarshe Haj Hauwa da Haj Sa’adatu sun yi kira ga al’ummar ƙasar nan su fito kwansu da kwarkwata don zaɓar Obi da Datti don kawo muku sauyi a kasa baki daya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
To mu dai a nan muna addu’ar Allah ya baiwa wanda suke da tunanin kawo mana mafita da cigaban kasar baki daya