Wasu Sabbin Abubuwa 7, Da Suka Fito A Gasar Kofin Duniya

created by Polish

Alfijr ta rawaito wasannin da Qatar ta dauki nauyin dauka na cin kofin duniya 2022, an samar da jerin wasu sababbin abubuwa da za a gani a gasar ta bana, wadda kasashe 32 za su fafata a gaban ’yan kallo kimanin 1.2 a Doha, babban birnin kasar Qatar.

1. Karon Farko A Gabas Ta Tsakiya:

 Wannan shi ne karon farko a tarihi da wata kasar Larabawa da ma daukacin yankin Gabas ta Tsakiya ta karbi bakuncin gasar cin Kofin Duniya.

2. Alkalan wasa mata:  

A karon farko mata za su yi alkalancin wasa a tarihin gasar.

An nada mata uku a cikin mutum 36 da za su yi alkalancin wasannin Matan su ne Stephanie Frappat daga kasar Faransa da Yoshimi Yamashita daga Japan sai Salima Mukansanga daga Ruwanda. Akwai kuma karin mata 69 da za su je gasar a matsayin mataimakan alkalan wasa.

3. Na farko a watan Nuwamba: 

Qatar 2022 shi ne gasar Kofin Duniya na farko da za a buga watan Nuwamba zuwa Disamba, sabanin na shekarun baya da aka saba yi a watan Yuni zuwa Yuli. An sauya lokacin ne domin guje wa yanayin zafin Qatar da kan kai maki 50 a ma’aunin selshos a Yuni-Yuli, zuwa Nuwamba/Disamba inda yanayin zafin ke komawa tsakanin maki 14 zuwa 31 na ma’aunin selshos.

4. Karin sauyin ’yan wasa: 

A karon farko kowace tawaga za ta iya yin sauyin ’yan wasa biyar a wasa guda, sabanin uku da aka saba yi a baya. Idan wasa ya shiga karin lokaci, an yarje wa kowane bangare yin sauyin dan wasa guda daya.

5. Karin ’yan wasa: 

An sahale wa kowacce tawaga tura ’yan wasa 26, wato karin mutum uku kan na gasar da aka yi a Rasha.

Haka ma an kara yawan ’yan wasan da za su gabatar na sharar fage daga 35 zuwa 55.

6. Na’urar gano satar gida: 

Za a fara amfani da wannan fasaha ta zamani da za ta gano, ta dauki hoton dan wasan da ya yi ta kuma bayyana domin ’yan kallo, har a gidajensu su gane dalilin da alkalin wasa ya yanke hukunci.

2. Tsukakken wurin gasa:  

Za a yi gasar ne a kasar mafi kankanta da ta taba daukar nauyin gasar ta FIFA a tarihi.

Dukkkanin filayen da za yi wasannin ba su da nisa da juna a birnin Doha mai fadin kilomita 50. Wasu filayen wasan za buga wasa a cikin har sau hudu a rana kuma ana hasashen samun cinkoso sakamokon halartar mutane kimanin miliyan 1.2.

 Aminiyi

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *