Alfijr ta rawaito Sama da fasinjoji 40 ne suka mutu sakamakon kifewar wani kwale-kwale da ke jigilar ‘yan kasuwa a kogin Neja da ke Bagana a karamar hukumar Omala ta jihar Kogi.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:12 na daren Lahadi, 18 ga watan Disamba, 2022, inda kwalekwalen da ke dauke da fasinjoji sama da 47 ya kife.
Wata majiya ta ce yawancin wadanda abin ya shafa ‘yan kasuwa ne kuma ‘yan asalin garin Umaisha ne, wadanda ke komawa Umaisha a jihar Nasarawa bayan sun je wata kasuwa da ke garin Bagana a jihar Kogi.
An bayyana cewa, kwale-kwalen da ke cikin sauri ya yi karo da wata bishiya da ke tsakiyar kogin inda nan take ya kife.
Majiyar ta kara da cewa dukkan mutanen da ke cikin jirgin ciki har da mata da kananan yara da ke cikin jirgin sun nutse.
“A gaskiya suna dawowa daga Bagana, kasuwar kauye ta kogin Niger suna komawa Umaisha, sai kwale-kwalen ya ci karo da wata bishiya a tsakiyar kogin, kuma kwatsam ya kife, an gano wasu gawarwaki, yayin da ake ci gaba da aikin ceto,” inji majiyar.
Ohimegye na masarautar Opanda-Umaisha, Mai Martaba Alhaji Usman Abdullahi, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a ranar Litinin.
Ya ce wadanda abin ya shafa mutanen masarautarsa ne, wadanda suka hada da wasu ‘yan kasuwa na Hausawa da ’yan fashi da ke dawowa daga kasuwar Bagana zuwa Umaisha.
“Har yanzu ban sami cikakken bayani da jimillar mutanen da hatsarin kwalekwalen ya rutsa da su ba.
Daya daga cikin mutanen fadara ne ya kira ni ya sanar da ni lamarin a lokacin da ba na nan,” inji shi. Sarkin, ya ce zai koma ga wakilinmu bayan ya isa gida domin jin cikakken bayani kan hasarar da aka yi a lamarin.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇