Wata Sabuw! Mazauna Jihar Lagas Sun Fara Yiwa Shugaba Tinubu Ihu

IMG 20231231 092350

Suna ihu da harshen Yarbanci, “Ebi npa wa oo” ma’ana- muna jin yunwa.

Alfijir labarai ta rawaito ranar Juma’a ne mazauna tsibirin Legas da ’yan kasuwa na babbar kasuwar Idumota suka nuna rashin gamsuwa da Shugaba Bola Tinubu, suna ihu da harshen Yarbanci, “Ebi npa wa oo” ma’ana- muna jin yunwa.

‘Yan kasuwar da suka yi wannan ihun a bangarorin biyu na titin yayin da ayarin motocin shugaban kasar suka bi ta kasuwar, sun ki yi masa jinjina amma maimakon haka suka ci gaba da magana kan radadin da suke ciki da ake kyautata zaton gwamnati ce ta janyo hakan.

A karkashin koke-koken da ke cikin faifan bidiyon, an ji mazauna garin na cewa fadar shugaban kasar ta san tsare-tsaren mutanen wanda shi ne ya sa aka dauki tsauraran matakan tsaro duk da haka, bai hana mutanen kasuwar nuna damuwarsu ba.

Shugaban ya je Legas ne domin bikin Kirsimeti da na sabuwar shekara.

Jama a da dama a fadin kasar sun ta kokawa da salon mulkin da shugaban ya fara wanda al ummar ke cewar, bayan fara tsunduma su da tsohuwar gwamnatin shugaba Buhari ta yi a cikin masifar rayuwa yanzu haka wannan ya zo ya karasa Danna su gaba Daya.

Allah ya ka wo mana sauki da rangeame Ameen.

DAILY POST

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *