Wata Sabuwa: An fita Da Zababben Shugaban Ƙasa Bola Tinubu A Asirce Zuwa Asibiti

Alfijr ta rawaito zababben shugaban ƙasar Tinubu, mai shekaru 70, zai iya sake samun kansa yana bayyana hakikanin yanayin lafiyarsa da ya dade yana jan hankalin jama’a masu kokwanto.

An fita da zababben shugaban kasa Bola Tinubu ya tafi zuwa kasar waje a wata ziyarar sirri da ya yi a cikin dare kamar yadda mukarrabansa biyu wadanda suka bayyanawa jaridar Peoples Gazette suka bayyana.

Abokan huldar sun ki bayyana kasar da aka kai Mista Tinubu, amma sun dage cewa ba ya cikin Mummunar jinya kuma nan ba da jimawa ba zai dawo kasar.

Sahara Reporters ce ta fara bayar da labarin tafiyar Mista Tinubu a ranar Laraba da yamma, inda kafar yada labarai ta yanar gizo ta ruwaito majiyar ta ta ce an kai sabon shugaban Najeriyar zuwa Turai domin jinya.

Sahara Reporters ta kuma ce Mista Tinubu, wanda aka ayyana a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar Najeriya a watan da ya gabata, ya kamu da rashin lafiya bayan shafe watanni ana gudanar da harkokin siyasa ba tare da katsewa ba, wanda ya kai ga karshen yakin neman zabe na shekara.

Bayo Onanuga, mai magana da yawun Mista Tinubu, ya fada a wani sako da ya aikewa jaridar The Gazette cewa shugaban nasa ya tafi kasar waje domin hutawa kuma nan ba da jimawa ba zai dawo kasar.

Mista Tinubu, mai shekaru 70, zai iya sake samun kansa yana bayyana halin lafiyarsa wanda ya jawo shakkar jama’a.

A cikin ‘yan shekarun nan, Mista Tinubu ya yi tafiye-tafiyen gaggawa da dama a kasashen waje, ciki har da a karshen watan Janairun 2022 da aka garzaya da shi Landan a lokacin da ake gudanar da yakin neman zaben fidda gwani.

A watan Satumbar 2022, Mista Tinubu ya sake komawa Landan, inda aka ce ya shafe makonni da dama yana karbar magani daga likitoci da dama.

Ya yarda a wani lokaci cewa yana iya rasa karfin jiki amma ya ce karfin tunaninsa zai isa ya tafiyar da al’amuran kasar.

Peoples Gazette

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *