Wata Sabuwa! Hisbah Ta Kama Wasu Masu Yin Balangu da  Mushen Rago A Kano

IMG 20231204 210431

Hukumar Hisbah ta yi nasarar kama wasu mutane da suke cin kasuwar mushen rago da kaji hadi dayin balangunsa.

Alfijir labarai ta kwamandan Hisbah na karamar hukumar Tarauni malam Nasir Adam Mai kaji yace dakarun Hisbah na karamar hukumar Tarauni ne su kayi nasarar kamo mutanen a daidai lokacin da suke yunkurin tafiya da naman mushen domin kaiwa kasuwa.

Kwamandan ya ce abin da takaici yadda mutanen da suke ikirarin su musulmi ne a ce suna ɗaukar mushe a bola su gyara da nufin sayarwa mutane wanda yin hakan ka iya jawo cutuka ga mutane wadanda ba za’a iya gane kansu ba.

Yayi kira ga al’umma da su himmatu wajen kai mushen dabbobinsu gidan kula da namun daji ko kuma su binne sh,i domin kaucewa bata gari kofar siyar da mushe ga al’umma.

Mutanen da aka kama Aminu Abdullahi da Isyaku Musa sun tabbas suna sayar da mushen ne a sabon gari, kuma masu amfani da mushen sukan basu kyautar barasa tare da biyansu kudade.

Sai dai Aminu da isyaku sun ce sun yi nadamar rungumar wannan sana’ar da suka dauki tsawon lokaci suna gudanarwa ba tare da an kamasu ba, sai a wannan karon sun kuma yi al’washin daina wannan sana’ar kwata kwata.

A nasu bangaren hukumar Hisbar ta umarci mutanen biyu su binne naman duk da wani balangun mushen da sukayi duk da sun bayyana cewa Suma su na cin balangun da sukayi da mushen.

Inda Ranka

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *