Wata Sabuwa: Muhuyi Magaji Ya Sake Kaddamar Da Sabbin Zarge-zarge Akan Ganduje

Muhyi magaji

Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta ce zata sake gurfanar da wani tsohon gwamnan jihar Abdullahi Ganduje bisa zargin almundahana da almubazzaranci da dukiyoyin al’umma.

Alfijir Labarai ta rawaito shugaban hukumar yaki da cin hanci, Muhuyi Magaji Rimin Gado ne ya bayyana hakan a cikin shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels Television a ranar Talata.

“Yanzu haka da nake magana da ku, muna kan binciken wasu kudin har kimanin N51.3bn wadanda gwamnatin tarayya ta turowa kananan hukumomi kuma aka dauke su daga asusun gwamnati aka aika wa wasu mutane, kuma mun gano mutanen da aka turawa din.”

Magaji ya yi zargin cewa a watan karshe na gwamnatin Ganduje ta kwashi Naira biliyan 1 daga asusun gwamnati, da sunan za’a yi aikin hanya da su, amma sai muka ga an tura da kudin ga wasu kamfanonin Chanji Kudaden kasashen waje.

“Muna da wata kara da muka shigar akan Naira biliyan 4, wadda aka fitar da ita daga asusun ajiyar kudaden shiga na jihar Kano zuwa wani kamfanin noma. Duk wadannan kararraki suna gaban kotu,” inji shi.

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa na Kano, wanda ya ce ana kallonsa a matsayin “mai taurin kai” saboda harkar halasta kudaden haramun batu ne da gwamnatin tarayya ce da hurumi akai, amma yace hukumarsa na da hakkin bincike akan zargin almundahana da ake yiwa Ganduje .

Magaji yace ya fara binciken gwamnatin Ganduje ne tun yana gwamnan Kano. Ya ce bai kamata a samu shafaffu da mai a yaki da cin hanci da rashawa a jihar ba.

“Abun dadin shi ne kyawun a Najeriya ba Wanda ya Isa yace yafi karfin a gurfanar da shi a gaban Shari’ar don haka kawai Ganduje ya shirya gurfana a gaban kotu domin ya kare kansa.”

Kadaura24

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *