Daga Aminu Bala Madobi
Babban Abin takaici da jin kunya da ya kusan faruwa a yayin da Mataimakin Gwamnan Bauchi yaso Sharara Mari Ga Ministan Harkokin Waje Yusuf Tuggar Cikin Mota.
Rahotonni Sun nuna cewa a ƙarshen mako nan manyan baki da mashahuran mutane ne da suka hada da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima da gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya su kaiwa fadar Sarkin Bauchi tsinke.
A ranar Asabar din ne dai aka samu wata hatsaniya tsakanin Auwal Jatau, mataimakin gwamnan jihar Bauchi da kuma ministan harkokin wajen kasar Yusuf Tuggar, lamarin da ya kai ga jami’an tsaron mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ne suka shiga tsakani don hana ruruwar fadan.
Sahara Reporters ta samu daga wata majiya mai tushe cewa arangama ta faru ne a cikin wata motar bus din da ta nufi fadar mai martaba Sarkin Bauchi wanda zata nada tsohon Gwamna Muhammad Abdullahi Abubakar a sarautar Babban Makama na 1 na masarautar Bauchi.
Babbar Motar mai dauke da manyan baki daga filin jirgin sama zuwa fadar Sarkin domin nadin sarautar, lamarin yazo daidai da bikin daurin auren yarsa.
Bikin dai ya samu halartar manyan baki da suka hada da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima da gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya.
“Matsalar ta faru ne a lokacin da Gwamnan Bauchi ya ke cewa Yusuf Tuggar, Ministan Harkokin Waje cewa shi (Tuggar) za a yi maganinsa saboda rashin mutunta shugabannin siyasar Jihar.
Hakan ya biyo bayan hango allon tallan sa ne a lokacin da suke cikin motar bas,” wata majiya mai karfi ta bayyana wa manema labarai a yammacin yau Asabar.
“Lokacin da Tuggar ya amsa cewa jihar ba ta wani bace shi kadai, mataimakin gwamnan ya tuhume shi daga bayan motar yana barazanar cewa zai yi wa Tuggar dukan tsiya, amma saboda ministan na zaune kusa da Mataimakin Shugaban Kasar, mataimakin gwamnan da ya zage damtse don kai masa naushi ya kasa isa gare shi, saboda jami’an tsaron da ke kula da Kashim Shettima,” majiyar ta kara da cewa.
Tawagar ta yi ta ihu – abin kunya ga mataimakin shugaban kasa – kafin su isa fadar mai martaba Sarkin Bauchi, inda kowa yayi shiru tamkar ba ayi ba.
Jim kadan da barin fadar sarkin, mataimakin gwamnan ya sake tuhumar Tuggar tare da barazanar cewa zai yi maganinsa.”
Hakan ya sa Tuggar bai bi ayari su shiga cikin tawagar da suka koma gidan gwamnati ba. An yi hakan ne don gujewa fafatawar da mataimakin gwamnan ya yi barazana
“Dan gwamnan Bauchin, Shamsudeen shine ya wallafa cewa mataimakin gwamnan ya mari ministan harkokin waje.”
A halin yanzu duk da kokarin jin ta bakin manyan hadiman gwamnan da ministan ya ci tura.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD