Wata Sabuwa! Yadda Wani likitan Masu Tabin Hankali Ya Sha Da Kyar Bayan Da Ya Sha Cizo

IMG 20240516 WA0070

Daga Aminu Bala Madobi

A daren ranar laraba wata tashin tashina ta barke a Asibitin kulada masu rangwamen hankali dake Aro, Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun, lokacin da majinyata da ke asibitin suka nuna rashin amincewarsu da abin da suka bayyana a matsayin ‘rashin nuna kukawa daga mahukuntan asibitin dake yi musu.

Alfijir labarai ta ruwaito a cewar rahotanni, wani likitan tabin hankali, wanda har yanzu ba a tantance ko wanene ba, da ma’aikatan jinya uku ne suka tsere daga hannun majinyatan da ke zanga-zangar. Sai dai cewa likitan ya samu cizon hakori daga guda cikin majinyatan.

Daga bisani jami’an ‘yan sanda daga hedikwatar sashin Lafenwa suka shiga tsakani suka shawo kan lamarin.

Bugu da kari, bayanai sun ce majinyatan na zanga-zangar nuna rashin gamsuwa da rashin ciyarwa, rashin tsaftar muhalli, da kuma rashin samun wutar lantarki, a duk lokacin da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta IBEDC ya yanke wutar lantarki.

Wasu ‘yan uwan ​​majinyatan da suka zanta da manema labarai sun ce an dade ana cikin irin wannan hali na rashin tabbas.

Sun ce hakan ya faru ne sakamakon rashin hanyoyin magance matsalolin.

Wata ‘yar uwan ​​daya daga cikin majinyatan da ta nemi a sakaya sunanta, ta ce mafi karancin kudin da kowannen majinyatan ke biya ya kai N500,000 zuwa N700,000.

Jami’in hulda da jama’a na cibiyar, Abiola Ajibola da ya ke magana a kan ci gaban, ya ce lamarin “al’amuran cikin gida ne kawai” da za a iya gyara shi.

Da yake magana kan lamarin, bayan samun amincewar kwamishinan ‘yan sandan jihar, Abiodun Alamutu, jami’in ‘yan sanda reshen Lafenwa, Enatufe Omoh, ya ce daya daga cikin likitocin tabin hankali ne aka ci zarafinsa ta hanyar cizon sa.

Ya ce likitan ya sami cizon hakora daban-daban daga masu fama da tabin hankali a lokacin da suke zanga-zangar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *