Wata Uwa Ta Rasa Ranta A Ƙoƙarin Raba Faɗa Tsakanin Ƴaƴanta A Abuja

Alfijr ta rawaito wata mata mai suna Zainab Ibrahim ta rasa ranta a kokarin raba fada tsakanin ‘ya’yanta maza biyu, Inusa da Usman.

Duk da cewa babu cikakken bayani kan abin da ya haɗa su, bayanai na nuna cewa Inusa ya soka wa mahaifiyarsa wuƙa a hannunta na dama bisa kuskure.

BBC Hausa ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a yankin Kpaduma da ke unguwar Asokoro a Abuja.

Wani mazaunin unguwar Saliu Shehu ya ce an gaggauta kai Zainab asibiti amma daga baya sai rai ya yi halinsa.

A lokacin da aka tuntube shi, mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda Abuja, Josephine Adeh, ta ce Inusa ya tsere amma ana bincike kan lamarin.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *