Yadda Babban Daraktan Hukumar Shari’a ta jihar Kano Dr Sani Ashir ya jagoranci buɗe Masallacin juma’a a garin Sane Bere dake ƙaramar hukumar Dawakin Tofa da naɗa limaman da zasu gabatar da sallah a garin.
An gudanar da sallar ne da misalin karfe daya da rabi 1:30 na wannan ranar ta juma’a bayan shekaru da wannan gari yake ta bukatar bude wannan Katafaren masallaci.
Al’ummar wannan gari mazansu da matansu yara da tsofaffi sun yi fitar dango domin shaida wannan ranar tarihi a garin.
Bayan huduba mai ratsa zuciya da babban malamin yayi, bayan idar da sallah an kuma yiwa babban limamin da zai jagoranci masallacin da Naibinsa da ladani nadi domin tabbatar musu da wannan aikin.





Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD