Yadda Diloli Suke hana Mu Sayar Da Buhun Siminta Akan N3,500 – In Ji BUA

Screenshot 20240830 190626 Facebook

“Diloli da dama sun yi amfani da damar da muka bayar ta karya farashin siminti don cimma manufarsu mara kyau. Maimakon su ƙara riba kaɗan a kan farashin da muka sayar musu, sai suka riƙa ninka farashinsa.”

Alfijir Labarai ta rawaito Abdulsamad Rabiu yace karyewar farashin Naira da cire tallafin man fetur su ma sun taimaka wajen rashin ɗorewar shirin nasa na karya farashin siminti.

Shugaban kamfanin BUA Cement Plc, Abdulsamad ya bayyana yadda diloli suka riƙa yin ƙafar-ungulu a shirin kamfaninsa na sayar da kowane buhun siminta a kan N 3,500 a bara.

Da yake jawabi a wurin taron shekara-shekara na kamfaninsa a Abuja ranar Alhamis, Abdulsamad Rabiu ya zalamar da diloli suka riƙa yi ta neman ƙazamar riba ce ta sa suka dinga ƙara kuɗi a kan farashin simintin.

A cewarsa, “Diloli da dama sun yi amfani da damar da muka bayar ta karya farashin siminti don cim ma manufarsu mara kyau. Maimakon su ƙara riba kaɗan a kan farashin da muka sayar musu, sai suka riƙa ninka farashinsa.”

“Wasu daga cikinsu sun riƙa sayar da kowane buhu ɗaya na siminti a kan N7,000 zuwa N8,000. Ba ƙaramin kuɗi suka samu ba. Ina tsammani mun sayar da fiye da tan miliyan ɗaya a kan N3,500 kafin mu fahimci abin da dilolin suke yi,” in ji shugaban kamfanin BUA.

Ya ce, “Mun so farashin ya tsaya a yadda yake amma diloli suka ƙi. Don haka, babu yadda za mu iya ci gaba da sayar da shi a kan wancan farashin domin kuwa tamkar diloli kaɗai muke bai wa tallafi.”

Abdulsamad Rabiu ya ƙara da cewa karyewar farashin Naira da cire tallafin man fetur su ma sun taimaka wajen rashin ɗorewar shirin nasa na karya farashin siminti.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *