Yadda Farashin Kayan Abinci Ke Gudana A – Kasuwar Damboa Dake Jihar Maiduguri

IMG 125130 19326 1773921098651

Daga Auwalu Tahamu Zarewa

Yadda take kasancewa a Kasuwar Hatsi ta Sabuwa  Karamar Hukumar Damboa LGA   dake Jihar Maiduguri Najeriya

Kasuwar Damboa ta nuna ƙarin tashin farashi a yawancin kayan gona a wannan makon, yayin da wasu kaɗan suka tsaya daram ko kuma suka sauka.

Hatsi (Grains & Cereals)

Masara (100kg): 24,000 (ba canji)
Dawa (100kg): 20,000 (ƙaruwa kaɗan)
Shinkafa (60kg): 31,000 (ƙaruwa)
Gero / Maiwa (100kg): 40,000 (ba canji)

Wake da Gyada (Legumes & Nuts)

Farin Wake Banjara (75kg): 76,000 (ƙaruwa)
Jan Wake (85kg): 65,000 (ƙaruwa)
Gurjiya / Bambara Nut (50kg): 35,000 (raguwa)
Gyada Sadiya (80kg): 78,000 (ƙaruwa)
Gyada Kamfala (80kg): 85,000 (ƙaruwa)

Ganyayyaki (Vegetables & Leaves)

Kuka (25kg): 12,000 (ba canji)
Kuka (19kg): 9,000 (ba canji)

Nazarin Kasuwa

A bangaren hatsi, shinkafa da dawa sun nuna ɗan ƙaruwa, yayin da masara da gero suka tsaya a farashin su ba tare da canji ba.

A bangaren wake da gyada, an samu ƙarin tashin farashi gaba ɗaya, musamman a wake da gyada. Sai dai gurjiya ta ci gaba da sauka.

Bangaren ganyayyaki bai nuna wani canji ba a wannan makon.

Hasashen Kasuwa

Cigaba da tashin farashin wake, shinkafa da gyada na nuna cewa buƙata tana ƙaruwa, musamman bayan lokacin azumi, tare da ɗan jinkirin wadatar kayayyaki a kasuwa.

Shawara ga ‘Yan Kasuwa da Manoma

A yi ƙoƙarin sayen wake da gyada da wuri saboda alamun ƙarin tashin farashi.

A yi anfani da saukar farashin gurjiya domin saye da yawa.

A ci gaba da siyan hatsi kamar yadda yake domin farashin su na daidaito, wanda zai taimaka wajen rage haɗarin kasuwa.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

Wahttps://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *