Yadda Kwastam ta kama makamai da ƙwayoyin na biliyan 10

FB IMG 1754988394515

Hukumar Kwastam Najeriya ta kama kwantainoni 16 ɗauke da makamai da miyagun ƙwayoyi da magungunan da wa’adin aikinsu ya ƙare da wasu haramtattun kaya na kimanin Naira biliyan 10 a Tashar Jiragen Ruwa ta Apapa da ke Jihar Legas a ranar Litinin.

Hukumar ta bayyana cewa ta kama mutane shida dangane da wannan haramtattun kaya da aka yi fasa-ƙwaurin su zuwa Najeriya.

Kwanturola Janar na Kwastam, Adewale Adeniyi, ya sanar da cewa an yi ƙarya wajen bayyana kayan da  kwantainonin suke ɗauke da su, inda aka ɓoye makamai, harsasai da magungunan da ba su da rajista.

“A yau, muna sanar da kama kwantainoni 16 da shigowarsu ke karya dokokinmu kuma suna barazana ga tsaron ƙasa. Darajar harajin da za a biya kan waɗannan kaya ya haura Naira biliyan 10,” in ji Shugaban Hukumar.

Fassarar Aminiya

For Advert Or Advice Call +2348032077835

For more information about Alfijir labarai/Alfijir news fallow here 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *